Hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta samu nasarar cafke wasu masu safarar makamai ga kungiyar Boko Haram, kamar yadda majiyarmu ta BBC Hausa ta rawaito.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar ta ce ta samu nasarar kame Musa Garba Abubakar, wanda aka fi sani da Musa bin Haddad a garin Jos da kananan bindigogi guda biyu, da albarusai da kuma wasu muhimman takardun bayanai na sirri.
Baya ga kera makamai da safararsu, a cewar sanarwar, Musa Abubakar ya je ofisoshin jakadancin wata kasa yana neman taimakon kudi da kayan aiki wa kungiyar Boko Haram.
Sanarwa ta ci gaba da cewa, hukumar ta kame karin wasu mutane biyu a kananan hukumomin Jos ta kudu da Bassa, duk a Jihar Plateau, masu taimaka wa Musa safarar makamai.
Title :
Hukumar SSS Ta Kama Masu Yi Wa Boko Haram Safarar Makamai
Description : Hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta samu nasarar cafke wasu masu safarar makamai ga kungiyar Boko Haram, kamar yadda majiyarmu ta BBC Hausa...
Rating :
5