Shugaban hukumar Kwatsam, Kanel Hameed Ali ya sake haramta shigo da shinkafa cikin kasar nan. Tare kuma da umartar a gaggauta rufe bakin iyakokin kasar.
Sanarwar hakan ta fito ne daga Kakakin hukumar na kasa, Wale Adeniyi inda yace an dauki matakin ne a lokacin wata ganawa da shugaban Kwatsam din yayi da manyan jami'an hukumar,
Sanarwar ta ce kudaden shiga da aka samu bayan janye dokar da aka sa a cen baya na hana shigo da shinkafar bai taka kara ya karya ba, wanda hakan ke nuna akwai ciwa-ciwa da fasa kwauri a ciki.
Sanarwar ta ce dokar ta fara aiki ne daga ranar 17 ga watan Maris da muke ciki, sai dai an yi rangwame ga wadanda suka riga suka sayo shinkafar kuma suke hanyar shigo da ita, da su kammala zuwa ranar Juma'a 25 ga watan Maris.
Title :
Hukumar Kwastan Ta Sake Hana Shigo Da Shinkafa
Description : Shugaban hukumar Kwatsam, Kanel Hameed Ali ya sake haramta shigo da shinkafa cikin kasar nan. Tare kuma da umartar a gaggauta rufe bakin iy...
Rating :
5