Gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin kafa kwamitin da za ta binciki manyan binciken da hukumomin EFCC da ICPC suka gudanar kan rashawa.
Kwamitin wanda yake a karkashin ofishin ministan shari'a, Abubakar Malami, za a yi masa lakabi da kwamitin shugaban kasa kan tantance kadarori.
Bincikenmu ya gano cewa kwamitin wanda har zuwa yau ba a kafa shi ba, za a kasafta shi ne gida uku.
Daya daga cikin kwamitin zai mayar da hankali ne kan kadarorin da kudaden da hukumar EFCC ta kwato, yayin da kuma dayan kwamitin zai binciki bangaren hukumar ICPC.
Kwamiti na ukun kuma zai gudanar da binciken sa ne a bangaren ma'aikatar fansho.
Title :
Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Kwamitin Da Za Ta Binciki Hukumomin EFCC Da ICPC
Description : Gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin kafa kwamitin da za ta binciki manyan binciken da hukumomin EFCC da ICPC suka gudanar kan rashawa. ...
Rating :
5