Gwamnatin jihar Kano ta cimma yarjejeniya da masu sayar da ledar ruwa (pure water) a jihar don ganin sun rage farashin jekar ledar ruwan daga naira dari zuwa tamanin. Wanda hakan na nufin za a dinga sayar da leda biyu na ruwan kan naira sha biyar, maimakon naira goma da ake sayar da duk leda guda kafin cimma yarjejeniyar.
Membobin kungiyar sun kuma sha alwashin dawo da farashin ledar ruwan zuwa naira biyar kamar yadda ake sayarwa a can baya, da zarar farashin ledar da ake zuba ruwan ya sauka.
Yayin da yake jawabi jim kadan bayan kammala taro da membobin kungiyar masu ruwan a gidan gwamnatin jihar, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana matsayar da aka cin mawa a taro kan matsalar hauhawar farashin ruwan leda a jihar.
"Gwamnati na sane da matsalar amma kuma a lokaci guda dole ne masu ruwan su duba yanayin", inda gwamnan ya kara da cewa ya tuntubi wani kamfanin leda a jihar Rivers, wanda ya yi alkawarin taimakawa dillalan ruwan don samun ledar su cikin farashi mai sauki.
Ya kuma kara da cewa gwamnatinsa ta sashen ma'aikatar muhalli za ta taimakawa dillalan ruwan da injinan hada ruwan guda goma wanda zai kawo saukin farashin ruwan a fadin jihar.
Gwamnan ya kuma kara da cewa akwai shirin da suke kokarin fitarwa matasa, inda wadanda suka amfana da shirin za su dinga tattara tsoffin ledojin da aka yi amfani da su don sake sayarwa da kamfanonin ruwan.
Tun farko, shugaban kungiyar dillalan ruwan ledan na jigar Kano, Salisu Sani ya bayyana cewa kara farashin ruwan ya samo asali ne bayan tashin gwauron zabin da kudin ledar zuba ruwan ya yi daga naira 570 zuwa naira dubu 1250. Ya kuma kara da cewa farashin ruwan zai dawo naira biyar kamar yadda aka sani da zarar an sauko da farashin kudin ledar.
Title :
Gwamnatin Kano Ta Shiga Batun Farashin Ruwan Leda
Description : Gwamnatin jihar Kano ta cimma yarjejeniya da masu sayar da ledar ruwa (pure water) a jihar don ganin sun rage farashin jekar ledar ruwan da...
Rating :
5