Gwamnatin Jihar Kaduna Karkashin Jagorancin Nasiru El Rufa'i ta yi afuwa ga wasu Fursunoni har guda 56, wadanda ke garkame a gidan Yari na garin Kaduna.
Lokacin da yake jawabi a wajen sallamar Fursunonin, Babban Alkalin Jihar Tanimu Zailani yace yin afuwa ga Fursunonin ya zama wajibi ta la'akari da yadda Gidan Yarin ya cika ya batse da Fursunoni ba masaka tsinke, wanda matakin afuwar zai taimaka wajen magance matsalolin dake addabar gidan.
Tanimu Zailani ya kuma yi kira ga Alkalan Jihar da cewar, su kasance masu yin adalci a cikin shari'o'insu ba kowane laifi bane za'a ce a garkame mutum, da akwai laifukan da ke bukatar yin nasiha ko horo, ko kuma cin tara ba mai tsanani ba.
A jawabinshi Kwantorolan gidan yarin Kaduna Abubakar Garba, ya jinjinawa gwamnatin El Rufa'i dangane da wannan mataki da ta dauka na yin afuwa ga Fursunonin, sannan yanyi kira gare su da cewar su yi kokarin sauya halayensu idan sun bar gidan Yarin domin kasancewa 'yan kasa nagari.
Kwantorola Abubakar Garba ya kara da cewar a bisa ga doka da ka'ida gidan yarin Kaduna ya kamata ya kwashi fursunoni 500 ne amma sai gashi ana loda masa Fursunoni sama da 1000, wanda wannan ba karamar matsala ba ce.
Cikin Fursunonin da aka sallama har da wata mata mai danyen goyo, wacce ake zaton cewa ta samu cikin ne tare da goyonshi da kuma haife shi a gidan yarin, sannan da wani mahaukaci wanda aka tabbatar da cewar tsananin azaba ce ta haukatar da shi, da kuma wani yaro wanda aka tabbatar da cewar bai balaga ba.
Binciken da RARIYA ta yi ta gano cewar da akwai tarin Fursunoni wadanda ke garkame a gidan Yarin Kaduna ba tare da sanin laifin da suka yi ba, kuma babu wanda ya sanar da su, yawa-yawansu suna tsare ne ba tare da wata takardar rubutacciya ba daga hukuma, suna daure ne kawai kamar awaki.
Source Rariya
Title :
Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Yi Afuwa Ga Fursunoni 56
Description : Gwamnatin Jihar Kaduna Karkashin Jagorancin Nasiru El Rufa'i ta yi afuwa ga wasu Fursunoni har guda 56, wadanda ke garkame a gidan Yari...
Rating :
5