Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi rashin mahaifiyarsa, Hajiya Fadimatu Umaru Ganduje a yau Juma'a.
A jawabin da Madakin Ganduje, Alhaji Sama'ila Umar ya fitar, marigayiyar mai shekaru 95 ta rasu ne da misalin karfe bakwai na safiyar yau.
Mahaifiyar gwamnan ta rasu ta bar 'ya'ya shida ciki har da Madakin Ganduje, Alhaji Sama'ila Umar, gwamna Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Alhaji Hussaini Umar Ganduje wanda shine babban sakataren cibiyar malaman makaranta ta jijar Kano da sauransu.
An kuma yi jana'izarta bayan sallar Juma'a inda manyan daga ciki da wajen Kano suka halarci jana'izar.
Source Rariya
Title :
Gwamna Ganduje Na Kano Ya Yi Rashin Mahaifiyarsa
Description : Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi rashin mahaifiyarsa, Hajiya Fadimatu Umaru Ganduje a yau Juma'a. A jawabin da Madakin G...
Rating :
5