An karbi daya daga cikin 'yan uwa kimanin 200 da sojoji suka kai kurkuku bayan harin da suka kai akan Harkar Musulunci a Zariya mai suna Malam Usman Zubairu Ikara a kan Beli. An karbi dan uwan ne a kan Beli saboda irin munin raunin da aka yi masa sanadiyyar harbin sa da bindiga da sojojin suka yi a unguwar Gyallesu sannan suka dauke shi suka jibge a kurkukun Kaduna ba tare da kula da yi masa magani ba.
Wannan yayi sanadin lalacewar hannun nasa har ya fara rubewa.
An bada Blin dan uwan ne a yau Talata 1 ga watan Maris bayan ya kwashe imanin watanni uku a gidan kason na Kaduna.
Ga wasu hotunan da aka dauka na dan uwan bayan an karbo shi:
Title :
Graphic Photos:An karbi wani dan uwa a kan Beli, saboda munin raunin sa bayan kusan wata uku
Description : An karbi daya daga cikin 'yan uwa kimanin 200 da sojoji suka kai kurkuku bayan harin da suka kai akan Harkar Musulunci a Zariya mai su...
Rating :
5