Dakarun sojojin Nijeriya na 155 Task Force Battalion dake karkashin 29 Task Force Brigade a yayin da suke kan farauta akan mahadar Banki a jiya Litinin, sun katse farmakin da 'yan Boko Haram suka kai musu a wani kauye da ake kira Bolungu, ìnda suka yi nasara akan 'yan ta'addan. Sojojjn sun kuma yi nasarar kashe uku daga cikinsu tare da kwato wasu bindigu masu lambar rijista kamar haka; UE16A86257 da wata kirar1G3 mai lamba 10f995, da wasu makamai da dama.
A wani labari makamncin haka kuma, sojojin sun yi artabu da wasu 'yan Boko Haram din a garin Manyati wadanda suka gudu daga sansanin su da aka fatattaka a wasu kauyuka, inda suke kokarin harbin sojojin, amma sojojin sun kashe daya tare da kama wasunsu. Daga cikin wadanda aka kama din yana kan bayyanawa sojojin wasu muhimman bayanai. An kuma gano kekuna biyar da buhunhunan hatsi da sauransu.
Haka kuma a wani labari makamancin haka sojojin a yau Talata sun sake tarwatsa sansanin 'yan Boko Haram din da dama a garin Gare dake kusa da Dajin Sambisa. A yayin artabun sojojin sun kashe dan Boko Haram guda daya, wanda ya kaiwa sojojin farmaki da adda, sannan kuma an kama hudu daga cikinsu.
Sojojin sun kuma ceto mutane 37 wadanda suka hada da maza 2 mata 9 da kuma kananan yara guda 26 tare kuma da gano wayoyi guda biyu.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin kakakin rundunar sojojin Kanal, Sani Kukasheka Usman.
Title :
Graphic Photos: Sojoji Sun Katse Harin 'Yan Boko Haram A Jihar Borno Tare Da Kashe Wasu 'Yan Ta'addan
Description : Dakarun sojojin Nijeriya na 155 Task Force Battalion dake karkashin 29 Task Force Brigade a yayin da suke kan farauta akan mahadar Banki a ...
Rating :
5