Kimanin mutane 18 ne suka rasa ransu, inda 17 daga cikin su suka kone kurmus a sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya auku a daidai wani kauye da ake kira Buzaye dake kan titin Bauchi da Jos, wanda ke da ratan kilomita 18 tsakaninsa da garin Bauchi.
Hadarin ya auku ne da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Lahadin da ta gabata, a yayin da birkin wata babbar mota da ta nufi garin Jos ya kwace, inda ya afka kan wata motar bas din Yankari mallakar jihar Bauchi mai dauke da mutane 18.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, Haruna Mohammed ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai a jiya, inda ya kara da cewa an kai gawarwakin wadanda suka mutu zuwa dakin ajiye agawa.
Kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da cewa babbar motar wadda kirar Daf ce tana dauke da lambar mota kamar haka; XC-675-BAU sai kuma karamar motar bas din tana dauke da lamba kamar haka; BAU-148-XR.
Ya kuma kara da cewa fasinjojin da suka kone sakamakon hadarin ba za a iya gane fuskokin su ba sakamakon mummunar kunewar da suka yi.
Saidai kakakin 'yan sandan ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda aka gane su a yayin hadarin sun hada da direban bas din mai suna Alhaji Adamu Maijama'a mai shekaru 45 daga garin Jahum a jihar Bauchi da kuma fasinja daya mai suna Yahaya Umar mai shekaru 41 daga Unguwan Dawaki a jihar Bauchi.
Kakakin ya kuma yi kira ga jama'ar da suka san wani na su ya yi tafiya daga Abuja zuwa Bauchi a wannan ranar da su je tashar mota dake Abuja domin bincike ko kuma su je asibitin koyarwa na jami'ar Bauchi don gano 'yan uwansu.
Title :
Graphic Photos: Mutane 18 Sun Rasa Ransu Sakamakon Hadarin Mota A Jihar Bauchi
Description : Kimanin mutane 18 ne suka rasa ransu, inda 17 daga cikin su suka kone kurmus a sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya auku a daidai wan...
Rating :
5