Kimanin mutane 20 ne rahotanni suka rawaito cewa sun rasa ransu sakamakon wani farmaki da wasu barayin shanu suka kai a wani kauye da ake kira Fanteka dake karamar hukumar Maru a jihar Zamfara. Wani mazaunin garin ne ya sanar da majiyarmu ta Blueprint hakan ta waya, inda ya ce 'yan bindigan wadanda sun kai dari, wanda kuma suka shigo kauye da misalin karfe biyu na dare akan babura a ranar Alhamis din da ta gabata.
Ya ce mazauna yankin sun yi nasarar kashe biyu daga cikin barayin shanun a yayin artabun, inda kuma ya kara da cewa da yawa daga cikin mazauna kauyen sun samu rauni a yayin da suke kokarin cetar da dayuwarsu.
Saidai wasu mazauna yankin sun dora laifin yawan kai hare-haren da 'yan bindigan suke yi ga jami'an tsaro da kuma gwamnatin jihar na rashin kawo musu dauki duk da cewa sun sha kai kukansu ga gwamnatin kan mawuyacin halin da suke ciki.
Sannan kuma an yi awon gaba da shanun mazauna yankin.
A yayin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Sanusi Amiru ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce rahotonsu ya nuna musu cewa mutane tara ne suka rasa ransu a yayin artabun, ciki har da barayin shanun guda biyu.
Sannan kuma ya kara da cewa tuni suka tura dakarunsu zuwa yankin domin ganin zaman lafiya ya dawo yankin. Inda kuma dakarun sojoji da na 'yan sanda sun bi sahun barayin don ganin sun kamo su.
Ya kuma yi kira ga jama'a da su kasance masu gaggawar sanar da jami'an tsaro game da mafakar miyagun mutane domin kawo daukin gaggawa.
Tuni dai aka yi wa wadanda suka mutu jana'iza a safiyar ranar Juma'a kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Title :
Graphic Photos: Barayin Shanu Sun Kashe Mutane 20 A Jihar Zamfara
Description : Kimanin mutane 20 ne rahotanni suka rawaito cewa sun rasa ransu sakamakon wani farmaki da wasu barayin shanu suka kai a wani kauye da ake ki...
Rating :
5