Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Najeriya na cewa wata gobara ta tashi a kasuwar Sabon Gari.Bayanai dai na cewa gobarar ta tashi ne tun tsakar daren jiya, kuma har yanzu tana ci ba a kai ga kashe ta ba.
Kawo yanzu dai ba a kai ga sanin musabbabin gobarar ba, babu kuma rahotannin hasarar rayuka ko jikkata.
Wannan na zuwa ne fiye da wata guda da wata gobarar ta tashi a kasuwar Singa mai makoftaka da kasuwar Sabon Garin duk dai a jihar Kano.
Title :
Gobara Ta Tashi A Kasuwar Sabon Gari A Jihar Kano
Description : Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Najeriya na cewa wata gobara ta tashi a kasuwar Sabon Gari.Bayanai dai na cewa gobarar ta tashi ne tun ...
Rating :
5