An Samu Gobara A Kasuwar Ikom Dake Jihar Cross River
Akalla shaguna 40 ne suka kone, a babbar kasuwar garin Ikom na jihar Cross River sakamakon gobara a kasuwar a jiya Talata.
Wutar dai wadda ta tashi da misalin karfe 2:00 na rana, an alkanta ta da matsalar wutar lantarki.
An ce jami'an kwana-kwana ba su iya kai dauki ba bisa korafin rashin kayan aiki.
Ko a karshen makon da ya gabata, kasuwar Sabon gari a Kano da babbar kasuwa da ke Birnin Kebbi na jihar Kebbi sun ci wuta, a inda kuma aka yi asarar dukiya mai yawa.
Title :
Gobara A Kasuwar Ikom Dake Jihar Cross River
Description : An Samu Gobara A Kasuwar Ikom Dake Jihar Cross River Akalla shaguna 40 ne suka kone, a babbar kasuwar garin Ikom na jihar Cross River sakam...
Rating :
5