Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a kokarin da yake na ganin kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ta zama tarihi a kasar nan.
Obasanji, wanda ya bayyana hakan a yayin ganawarsa da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima a garin Maiduguri a yau Litinin, ya kuma kara da cewa kasancewar yawaitar nasarar da dakarun sojojin ke ci gaba da samu a kan 'yan Boko Haram din a yankunan jihohin Arewa maso Gabas, musamman ma jihar Borno, nan bada jimawa ba 'yan ta'addan za su zama tarihi a kasar nan.
Ya ce duk da cewa har yanzu ba a ga bayan 'yan Boko Haram din ba, amma yana da yakinin cewa sun kusa zama tarihi a kasar nan.
Title :
Gaskiya Buhari Ya Yi Matukar Taka Rawar Gani Wajen Yakar Boko Haram - Obasanjo
Description : Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a kokarin da yake na ganin kungiyar ta'addanci ta Boko ...
Rating :
5