Bayanan da muke samu na cewa gwamnatin Kano karkashin Umar Ganduje na shirin kai sanata Kwankwaso gaban hukumar EFCC kan batan wasu makudan kudi lokacin da yake gwamnan Kano daga 2011-2015.
Bayanai masu karfi na cewa gwamnatin Ganduje ta fara bincike kan badaƙalar kuɗin ɗalibai da suka tafi kasar Jodan koyan tuƙin jirgin sama, bayanai na cewa Kwankwaso yayi hafzi da Naira biliyan 1.1 wanda daga karshe ta tabbata ake zargin sanata Kwankwaso da wawushewa.
Majiyarmu ta kuma samu labarin cewa hatta makarantu da Kwankwaso yayi na wasanni, sadarwa, koyar tuƙinn mota ance gwamnatin Kwankwaso ta kwashi makudan kuɗi fiye da Naira biliyan amma ba a kai kayan aiki cikin makarantun ba duk da cewa Kwankwaso ya karɓi kuɗin.
Bayanan da majiyarmu ta samu ya kuma ce yace hatta titunan mai tsawon kilo mita 5 da gwamnatin Kwankwaso ta dakko a kowace karamar hukuma an fitar da kuɗin kuma a wasu gurarenma ko farawa ba a yi ba.
Bayanai na cewa a halin yanzu gwamnatin ta Ganduje na hasale da yadda Kwankwso ya tafi ya barwa jihar Kano bashi har na fiye da Naira biliyan 350 wanda makusantan gwamnatin ke cewa hakan ya hana Ganduje aiki sosai wata 9 da ɗarewar shi kan kujera
Title :
Ganduje Na Shirin Kai Kwankwaso Gaban EFCC
Description : Bayanan da muke samu na cewa gwamnatin Kano karkashin Umar Ganduje na shirin kai sanata Kwankwaso gaban hukumar EFCC kan batan wasu makudan ...
Rating :
5