Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kiraga bankuna da su kara taimakawa wajen bayar da rance ga bangaren noma, a wani kokari da
gwamnati ke yi na farfado da tattalin arzikinta sakamakon faduwar farashin man fetur.
Wannan yunkuri ya biyo bayan kokarin da shugaba Buhari ke yi na ganin ya samar da wasu hanyoyin samun kudin shiga baya ga bangaren man fetur.
Shugaba Buhari ya shaidawa majalisar tattalin arzikin kasa cewa, "Babbar hanyar arzikinmu ita ce noma da kiwo."
Ya kara da cewa, "Don haka dole bankuna su kara yawan kudaden da suke bai wa manoma rance. Kuma babban bankin kasa zai kasance mai bayar da lamuni na basussukan a matsayin tsarin kasa."
Shuga Buhari ya kuma kara da cewa gwamnatinsa na shirin kara megawat 10,000 na wutar lantarkia kasar nan da shekaru uku da suka rage masa a kan mulki.
Title :
Buhari Ya Bukaci Bankuna Su Baiwa Manoma Rance Domin Bunkasa Harkar Noma
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kiraga bankuna da su kara taimakawa wajen bayar da rance ga bangaren noma, a wani kokari da gwamnati ...
Rating :
5