Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya bayyana cewa yadda Buhari yace ba zai iya biyan Naira 5000 ga matasan da yayiwa alkawari ba ya nuna cewa ya damfari 'Yan Nijeriya.
Fayose ya kuma bayyana cewa gaba kadan wata rana ma Buhari zai iya karyata duk alkawarurrukan da ya dauka wa 'yan Nijeriya.
Fayose ya kuma ce wata rana ma Buhari zai iya cewa ba talaka bane ya zabe shi ba shi ya zabi kansa, saboda haka ba wani alkawari da yayi wa talakan Nijeriya.
Fayose ya kuma ce wata rana Buhari ma zai iya cewa ba APC ce ta fitar da shi ba saboda munafurci irin na shi a cewar Fayose.
Title :
Buhari Da APC Sun Damfari Yan Najeriya - Fayose
Description : Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya bayyana cewa yadda Buhari yace ba zai iya biyan Naira 5000 ga matasan da yayiwa alkawari ba ya nuna ce...
Rating :
5