Budaddiyar wasika zuwa ga maigirma govnan jihar Bauchi Muhammadu Abdullahi Abubakar da mukaddashin govnan jahar Bauchi Engr Nuhu Gidado kashi na uku.
Assalamu Alaikum.
Ya maigirma Govnar jihar Bauchi tare da mukaddashinka dalilin sake rubuta maka wannan budaddiyar wasika shi ne don mudada jawo hankalinka kan abubuwan da suke faruwa da wanda ake tsammanin faruwarsu a jiharmu ta bauchi.
Ya maigirma govna muna dada jawo hankalinka ne ba dun komai ba sai don kalubalen dake gabanka a jihar bauchi don neman mafita domin jihar bauchi, jihar muce gaba daya.
Ya maigirma rawafa ya zamo dole ya chanza domin kidan ya fara chanzawa harma sautin kidan amfara barin jinsa.
Kadan daga cikin abunda ke faruwa a bauchi kuwa su ne:
Yadda kake gudanar ko kake jan ragamar mulkinka dayawan mutanen bauchi su na ganin akwai kura kurai masu yawa tattare dakai, na farko suna ganin aikin da kabayar na gyaran titi daga CBN roundabout akawai abun dubawa da nazari akai, domin yawancin al'ummar wannan jahar suna ganin bashi ne jamma'a suke bukataba ayanzu wasu kuma sunan ganin hakan (misplacement of priority ne) domin da'a kashe wannan tsununin kudi gara a gyara hanyar wanda kiyashi ya nuna cewa (renovation) din hanyar yafi zama dole kuma kudin da zaa kashe wajen gyaran bai uce milliyan dari biyoba har dayin magudanar ucewar ruwaba. Kuma fadada titin izuwa railway bashi da wani amfani don ba hanyace wanda ake kaikoma akansa dayawa ba, wato ba (busy location ba ne). Suna ganin kudin da zaayi wannan hanya gara ace ankasheshi ne wajen gina asibitochi a kauyuka koda ace (dispensaries) ko (maternities) ko kuma (health care centres) a duk fadin jihar. Wato kowani local government kenan.
Magana na biyu itace bada aikin gidajen da matan ka zasu zauna su biyu akimanin kudi wajen biliyan biyu shima abun dubawane maigirma govna. Tambayar dasukeyi shi ne wai ayadda kake yawanyin kukan rashin kudi yaya zaace kabada wannan tsununun kudi wa matanka biyu kachal? Wai shin bukatun matayenka yafi bukatun sauran matayen jahar bauchi ne? A ganinsu da tunaninsu yin hakan kuskurene babba, don dayin hakan gara ansa kudin a wajen ceto rayuwar al'umma na kunci, yunwa da talaucin da ake fama dashi.
Sai kuma batun aikin zaranda hotel daka ba dashi, shi ma al'umma suna ganin bashi muke bukataba ahalin damuke ciki a yau, domin da yin hakan suna ganin akwai alkawarurkan daka dauka lokacin neman yakin kuri'a dashi kasauke da yafi.
Ga kuma biliyan daya dasukace kasa a cosmopolitan wanda shugaban gurin sunce wai dan'uwankane kuma basuga wani aikin da'akeyiba, duk wai acikin kukan babu kudi dakake ta cewa.
Har batun rushe hakimannan wasu suna ganin kara zafine akan zafi gareka ya maigirma, atunaninsu dayin hakan gara a duba wadanda ba'ayisu akan ka'idaba a gyara, inkuma kudin albashinsu ne yayi yawa toh sai maigirma govna ya rage zuwa mafi dai dai. Domin rushe wadannan hakiman ya maigirma govna zai iya sa wasu da yawa bazasu koma ba kuma rashin komawar wasunsu zai iya jawo sanadiyar mutuwar wasu, don haka maigirma govna yayi dogon nazari.
Bayan haka ya maigirma govna akwai korafi da yawa akanka cewa akwai al'umma da yawa dasuka sha maka wahala amma kamanta dasu kakasa tsinana musu komai kabarsu da yunwa da bakin ciki duk injisu, don haka maigirma ya dubesu da idon Rahma.
Ya maigirma govna, masu kare muradunka sukan rasa mai zasu ce wa al'umma don basu da masaniyan mai govnati take ciki, ina ta sa gaba kuma mai take shirinyi agaba duk atunaninsu kabar komai gareka, babu mai iya baka shawara, wai kuma kasan komai, sabanin tunanin cewa govnati ta'uce mutun daya, don haka muna kiran maigirma govna da yabasu hadin kai don su samu abunda zasu iya gaya wa al'umma yadda govnati tasa gaba kuma mai take son ta cimma.
Ya maigirma govna anatacewa babu kudi a jihar bauchi amma sai gashi duk watan duniya ana wai ware ma gidajen matanka biyu miliyan asirin asirin ko mene ne gaskiyar wannan maganar? Na biyu kuma wai mai lura da aikin zaranda hotel abokin yayanka ne suna ganinma aikin nasune shi kawai frontie ne?.
Anatace babu kudi amma wai akwai wani jammi'i a govnatin ka wanda kasa aka biyashi bashin kwangilan dayayi tun 2013 kimanin kudi miliyan sittin ko mene ne gaskiyar maganar?
Bayan haka ya maigirma govna masu hangen nesa suna ganin kamar haryanzu ka kasa gano matsalar wannan gari tamu wajen samarda ingantaccen turba mai dorewa, domin akwai tsofaffin anguwanni kamarsu anguwan dim, malan goje, doya, gallaga, Tura, tuji, bakaro , jahun da dai sauransu suna bukatar aceci rayuwarsu wajen yimusu magudanar ucewar ruwa da fadada hanyoyin anguwannin don samun ingantaccen rayuwa wanda hakki ne arataye awuyarka, har ila yau cututtuka na cizon saura, tifod fever da kwalara ya addabesu don kwatamin da yake wayo a anguwannin sun.
Ya maigirma govna daga cikin abunda zaisa garin bauchi tasamu dan hada hada shi ne wajen kai hanyoyi guraren da aka yanka filaye wanda titi bai kai gurarenba shi yasa filayen suka kasa yin daraja don ba hanyoyin da mota zata iya ucewa. Kamar su tambari tsallaken gada, gida dubu wajen hanyan da tayi gubi, hanyan inkil zuwa kwata, Ibrahim bako anguwan sarki da kuma makamantansu. Wanda Samar musu da tituna zai dan agaza wa filayen su danyi daraja.
Daga karshe ina kira ga mai girma mukaddashin govna jihar bauchi Engr Nuhu Gidado daya dan fito fila wa jamma'a don korafi ya fara yawa akansa har mutane ma sunacewa sardaunan dasuka sa ni yanzu ya chanza.
Dafatan Allah shi bawa maigirma govna da mukaddashinsa sauke wannan nauyi daya daura musu, Allah kuma shi basu ikonyin aiki ajihar Bauchi wanda tarihi bazai manta dasuba, Allah shi sa su wanye lafiya, Ameen.
Aminun Bauchin Bauchi
Title :
Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamna Jihar Bauchi
Description : Budaddiyar wasika zuwa ga maigirma govnan jihar Bauchi Muhammadu Abdullahi Abubakar da mukaddashin govnan jahar Bauchi Engr Nuhu Gidado kash...
Rating :
5