Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne a jiya Laraba sun sun sace mata 16 a wani kauye da ake kira Sabongari dake garin Madagali a jihar Adamawa.
Wasu mazauna yankin sun bayyanawa majiyarmu ta Daily Trust cewa matan sun je kamun kifi ne a rafin Magar tare da rakiyar wasu matasa a lokacin da wasu matasa kusan su takwas rike da bindigu suka yi awon gaba da su.
Matasa biyun da suka raka matan sun tsira inda dayan ya tsira da harbin harsashi, yayin biyu daga cikin matan su ma suka tsira inda suka dawo kauyen.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Othman Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya kara da cewa sun aika da dakarunsu yankin.
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Michika da Madagali a majalisar wakilai ta tarayya, Adamu Kamale ya koka kan yadda jami'an tsaro suka yi karanci a wasu kayyukan da ke garin na Madagali.
Title :
Boko Haram Sun Sace Mata 16 A Garin Madagali
Description : Wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne a jiya Laraba sun sun sace mata 16 a wani kauye da ake kira Sabongari dake garin Madagal...
Rating :
5