Mabiya akidar Shi'a ta musanta rahotannin da ke cewa tana shirin yin tarzoma a duk fadin kasar nan.
Wata sanarwa da babban jami'in watsa labarai na kungiyar, Ibrahim Musa, ya fitar ta ce labaran da ake watsawa cewa suna shirin yin ramuwar-gayya bayan artabun da suka yi da sojojin kasar a garin Zaria a shekarar da ta gabata, karya ce tsagwaronta.
Sanarwar ta kara da cewa,"An gina labarin ne kawai kan wasu kalamai da wani dan uwanmu ya yi, kuma ba a fahimci abin da yake nufi ba."
A cewar Ibrahim Musa,"Muna so mu bayyana cewa babu kanshin gaskiya a kalaman da ake yi cewa muna shirin kai wa sojoji da ma sauran jami'an tsaro farmaki".
A watan Disambar shekarar 2015 ne rundunar sojin Nijeriya ta yi zargin cewa kungiyar ta 'yan Shia ta yi yunkurin kashe Babban Hafsan Sojin kasa na kasar, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, a lokacin da ya kai ziyara a birnin na Zaria.
Sai dai kungiyar ta 'yan Shia ta musanta zargin, tana mai cewa sojojin ne suka far ma 'yan kungiyar.
Lamarin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa kwamitin da zai yi bincike kan lamarin, ko da ya ke a makon nan 'yan kungiyar sun ce ba za su sake halartar zaman da kwamitin ke yi ba sai an sako shugabansu Sheikh Ibrahim Al-Zakzaky da wasu 'yan kungiyar da ake tsare da su.
Title :
Ba Mu Da Niyyar Tada Tarzoma, - Yan Shi'a
Description : Mabiya akidar Shi'a ta musanta rahotannin da ke cewa tana shirin yin tarzoma a duk fadin kasar nan. Wata sanarwa da babban jami'in...
Rating :
5