*** BA BAIWA BACE PART 5 ***
******* KARSHE *******
.
Juyawa dan ganin suwaye Hassan ne ya shigo tareda iyayensu amma banda hajiya zuwaira da sauri umma ta karasa wajen zara dan bata ma lura da suh mami dasuke wajen ba karasa wah tayi wajen gado zara ceh wlhy alhaji wlhy itane magana take kamar wata maral lafiya ihutake sanda likitoci suka kama ta aka mata aluran bacci dan tasamu bacci sai wajen mangariba sannan umma ta farka bata mawa kuwa magana ba gadon da zara take taje ta xauna kallon ta take kuwa a dakin kallon ta yake dan gani mai zatayi,yayah (haka take ki kiran ta) ta mutune ko tana raye, tana da rai, yaya ina kuka samu ta nan take hauwa ta labarta masu komai har izuwa rashin Period dinta shiru daki akayi wanda kuwa da abinda yake sakawa umma ne ta kara kama hanun zara tareda fadi allah xai saka maki ,knockin akayi nurse ce ta shigo tace doc ankawo maral lafiya mikewa yayi dan ko shima jikin sa yayi sanyi dan bai taba sammani karamal yarinya kaman wannan xatana fama da rashin lafiya haka dai yaje ya dawo a dakin dan kawea ya tabbatar data farka.yau kimani kwana3 kenan amma bata farka ba. Jabir ne yake xaune a dakinsa amma gaba daya ya kasa samun nutsuwa dan shi yana san zara tin nanda ya ganta a yake jin sonta amma ya kasa fada mata, yana xaune a dakin shi da abinki shi ahamd yake cemasa, abokina lafiya ka rame ka zama haka wlhy ahmad ina santa wlhy ina santa tin baxan ita waye bane, hassan ne yaxo zai shiga dakin jabir din yaji kaman ana magana muryan jabir yaji yana cuwa "wlhy ahmad ciwon xuciyan da ka rakani wajen doc yace ina da shi wlhy fateema zara ce sanadin dan wlhy ina san ta kuma na rasa yarda zanyi na fada mata dan ynxu naga akwea wani suraj da yake xuwa gidan nan naga yana santa kuma ga big bros mah yana santa duk da shi ba fada ba.ajiyan xuciya hassan yayi ya kuma fasa shiga dakin.
.
Ayau zan koma bauchi da sai murna nake ko ba komai xanje naga gidan muh, tin karfe 10na safe muka kama hanya amma bamu samu halin isa ba sai5 na yamma, muna isa yayi daidai da fitowan hajia Zuwaira itada kawarta hajia Nuriyat bude murfin kofa nayi yayi ko daidai da dagowan ta hada ido mukayi waye wannan kaman fateema murmushi abbu yayi itace mana kina mamakine bai gama rufe bakiba hajia xuwaira ta fara wlhy karyane va yarda za ayi fateema ta dawo dan ko boka ya fadamin va xata kara dawo wah ba nan ta zaiyane komai da tayi harda ko yankan farce da rashin alada ta hauka ta fara wanda yabawa kowa Mamaki. Ita ko hajia Nuriyat tana gani naka na faruwa motar ta ta shige ta fita daga gidan tana dariyan mugunta allahamdulilah Zuwaira sai yau burina ya cika akan ki ta fito daidai kan hanya ta farajin motar na hayaki kafin ta kokari fita har ya kama da wuta mutane son taru a wajen dan kashe wuta amma ina kama kara masa yayi ake sanda ya kone kumus kafin nan da kansa ya mutu dako aka duba ba gawan hajia Nuriyat balle aga wani abu dayayi kama da muutun ita ko hajia Zuwaira fita tayi daga gidan tana tafiya tana zaiyane duk avin da tayi a rayuwanta . ara tin da asuba dana farka nake fama sanda gari ya waye umma ta shigo ta gan ni a kwance lafiyan ki kuwa zara umma cikina a lokaci su abbu suke shigowa da sauri abbu ya karasa lfy meyasa meki cikina abbu zan mutun dawo ni yayi jini suka gani wanda duk ya bata kan gado harma da kayan jikina, umma ne tace abbu jini alaada ce bari kai ta bayi na wanke ta dagani abbu yayi ya kaini bayi umma taxo ta kyarani ta barni nayi wankan taxo ta gyara kan gadon nayi wanka naji dadi jikina bayan na fito pad nasa sannan nasa kaya kamani tayi muka sauko yareema umar ne shida jabir da sauri hassan yazo ya rikeni ya taimaka min xa zauna shiya bani abinci abaki har na kushi.
.
Umar ne yace abbu lafiya meyasame ta nan umma tace masa MP ke damuna kunya ce ta rufeni mikewa yayi yazo kusa dani in yake maki ciwo kama min hanu yayi abin ya mugun batawa jabir rae mikewa yayi yavar falo duk da hassaan na sane da shi. Fita yayi ya koma cikin mota yana rige da kirjin shi hassan ne ya bi bayan sa dan yasa hala ne ya iya tuki haka ko yana zuwa ya same shi a zaune a cikin mota kama hanun sa yayi bai masa musu ba ya visa side dinsa hassan ya nufa da shi dan shi har ga allah ya fi son jabir ya aure zara akan wani namiji a duniya, ruwa mai sanyj ya dauko ya basa kafa goran yayi a bakin sa sanda ya sanya kwanta wa yayi akan gado bacci ko ya dauke sa gyara mai kwanciya hassan yayi yana cike da tausaya masa dan ko ba komai shiya rike shi lokacin da ya je karatu hasali ma dakin suh daya dan sauran dukan suh tare suke kwanan shiko umar kallon ma bai ishe saba shiyasa yafi son jabir din kasa komawa yayi falon shiko umar sai wani shishige mata yake ,sai bayan kusan laasar jabir ya farka yadan ji sanyi a rae sa , hassan ne ya fito daga toilet alaman alola yayi kallon sah jabir yayi alaman mamaki bros kenan ka daina mamaki nasan halin da kake ciki yaya nasan kana fama da ciwon zuciya kuma sana diyan zara ce kallon sa yake ka tashi kawea mu tafi masalaci jiransa yayi har ya fito sannan suka nufi tare sanda suka idar ya dube shi hassan ina ka samu wannan labari murmushi hassan yayi sannan yace naji lokaci da kake fadawa abokin ka ahamd ajiyan zuciya yayi yace wlhy ina san zara amma nasan vazan same taba dan ko yaya yana santa kaga ko baxai yuba na furta hakan koda son zara zai xama ajalina , insha allah zara zata xama matan ka adua kawea zakayi dan ko matar mutun kabarin sa hakane kam haka suka karasa ciki kowa da abinda yake sakawa. Da suka shiga basu ga motan umar ba kenan ya tafi ciki suka shiga nan suka saneni da alamin muna cin abinci zama suka suma hassan ne ya fara magana sis ya jiki da sauki allah kara sauki amen na fada kallon jabir nayi yayana lafiya kuwa dagowa yayi me kika ga naga kaman kana damuwa ke kika sani a cikin damuwa, ni kuma zancen xuci yake amma ya fito fili ,wayancewa yayi eh mana bakida lafiya dole na shiga damuwa ayyah yayana ae na warke kallon ta yake da gaske kin warke murmushi tayi har sai da dimple dinta ta fito sun dan taba hira kafin ya mike ni xan tafi ko abbu ne ya shigo ina xaka kuma kaduna zan wuce ynxu eh karfe 5 ne fa kawea ka bari sai gobe amna ba yau ba badan yaso ba dan bai so yana kallona dan baya jin xai iya cigaba da kallon na ahaka.
.
Jabir ya koma da sati daya na damin abbu akan ina son naje kaduna haka ya barni dan ko dama shima yana so yaje dan mai martaba yana nemansa mun isa sai murna muke nida hauwa dan ko ynxu mun xama dYa , mufeeda kuwa dama anje an sawo mahaifiyarta ynxu ta dawo fada da zama . Mai martaba ne ya aika a kirawo muh dukan muh palon sa bayan ya buda taru da adua kuma akadan yi wasa da daria, gyaran murya yayi tareda duba dukan kafin nan yace kai jabir ina umar yake,rae ka ya dade inaga yana dakin kinshi umar ne ya shigo bayan ya mika gaisuwan sa zama yayi a gefan jabir mai martaba ne ya fara magana dalili dayasa na taraku anan dan ku yaran nan wato jabir,umar, hauwa, fateema, zarau,da kuma amira.lokaci yayi daya kamata ace kunyi dan haka ne yasa muka yanke shawaran hadaku wato kai jabir xaka aura fateema, kai kuma umar zarau xaka aura sauran hauwa da amira kuma sai ku turu wanda kuke so dan a lokaci daya za a hada ku. gaban zarau ne ya fadi ita gaskiya bata san umar hasalima haushin sa take ji ,umar kuwa murna yake dan shi na san ta haka dai tarun ya kare kuwa da avinda yake sakawa. Jabir bangaresa ya koma amma da kyar ya iya takawa zuwa wajen kan gado ya fada yana mai mayar da nufashi hassan da salim ne suka shigo daki da sauri suka kama sa suka kaisa cikin muta basu tsaya sanar da kuwa ba suka fita kai tsaye asibiti suka kaisa amma kafin suje wajen ya suma. Taimakun gangawa likita suka shiga masa amma sanda suka kai awa2 kafin suka samu ya dawo daidi wayan salim ne ya fara ringing hauwa ce take kiran sa dauka yayi tareda da yi shiru ita ta fara magana helo kana ina, muna asibiti, waye bai da lafiya salim anan ya fada mata meke faruwa kuma ya fada mata asbitin da suke amma karta sanar da kuwa, haka ko tayi ita da zarau ne kawea suka je koda sukaje bai farka ba.zarau da hauwa ne suka zauna a wajen yayin su kuna mazan suka koma gida. suraj ko daya samu labari bada zarau ya hakura amma badan ba yarda ya iya hajia babba ne ta same sa akan meyasa baxai soh hauwa tinda ita ma tana da hali mai kyau haka ko akayi kai tsayan wajen mai martaba akaje kuma ya amince ahaka aka tsayar da maganan nan da wata daya .
s Sanda jabir yayi kwana1 kafin ya fardado hassan ne da salim kawea a dakin mikewa yayi amma jiri ya mayarda shi tsakani shekara jiya zuwa yau ya rame kaman wanda ya shekara yana jinya,shida hassan ne kawea suka san meke faruwa sanda salim ya fita jabir yace wah hassan ina fatan baka fada wah kowaba eh kawea yace, kama hanun hassan yayi ina san dan allah kar ka bari kowa ya sani to kawea yace amma yasan dole wataran zai fada. Suh mami ne suka shigo a rude suke tmby meya faru doc ne ya fada masu cewa jabir na fama da ciwon xuciya kuma ciwon yayi tsanani a jikin sa, jabir ciwon xuciya fa suka ce me ya sameka da baxa ka iya fada mim ba ni da nake uwarka, ko me ka ke tunani da har ya haifarma wannan ciwo kuka mami ta fara wanda yasa mai mar taba cewa a mayar da ita gida. Biki sai matsowa yake ciwon jabir kuwa sai karuwa yake hakane yasa doc ce masu akan yana yawan gani abin baci rae ko kuma avin da ya hadasa masa ciwon tmby sai mami tayi akan ya fada ko ma meye dan a magance matsalan amma yayi shiru.an dauko masu gyara sai gyara amare ake duk da kowace ba tada xabi akan haka hauwa mah ana gyara ta amma da ta tmby mami ce mata akayi yana da kyau agyara mace ko bako aure xatayi ba. Ayau aka taru dan daurin aure wanda ya samu halarta manya mutane garu ruwa.karfe 11:00am aka hada auran umar Alkasim&fatema Salisu, Jabir Alkasim &Fateem zara Sulaiman da kum hauwa &suraj tinda aka shaida auran umar ya birkice akan shi an masa musayan mata ba fateema salisu ya kamata a hada sa da ita ba, shi ko salim yana jin haka asibiti ya nufa yaje ya rugume jabir am happy for u bros finally yau zarau ta zama matar ka kallon sa jabir yake, mikewa yayi ya nufa toilet kuka yayi kaman karamin yaro kuma ya hakura da zara tin da ynxu ta zama matar wani .
.
Dauri aure kawea akayi dan ko mai martaba ya hana dadin abin dukan suh ba so suke ba iya fateema da taji lbr daura mata aure da akayi da umar dinta kuma tayi alkawari koya masa son ta ko ta halin yayi. An salame jabir a asibiti danko ynxu ya fara samu sauki da dadare aka shirya amare aka kaisu gida jen maxa jensu hauwa ne kawea aka tafi da ita gombe tin da safe , gida ne mai kyau gaske dan tsayawa yaban kyau gidan bata lokaci ne.harga allah nafi son ya jabir sau dari akan umar danko dana ji hadin auran na ji dadi sosai sai kusan 11 ya shigo salama yayi amma na kasa amasawa xuwa yayi ya ajeye ledan daya shigo da ita.bude fuska yayi danko yayi alkawari zama da ko wacece aka hada shi da ita fuskan zarau ya gani da sauri ya mike kiyi hakuri na dauka gidana naxo ashe gidan umar ne mikewa nayi na kama hanunsa ya jabir nice matar ka zarau kin yarda yayi fita daga dakin yayi wayan sa ya ciro ya kira hassan, helo ango kai hassan hussaina fa nagani a gidana eh itan ce matar ka nan ya fadama sa komai lokacin danaga ciwon ka yayi tsanani yasa na samu abbu da mai martaba na fada masu halin da kake ciki ajiyam xuciya yayi tareda da kashe wayan gabar ya duba tareda yi sujada dan ya godewa allah sanda yakai kusan minti4 ahaka kafim ya mike ya nufi dakin da nake.
.
Fateema,zarau, hussaina ynxu ke mata nace na jima da yi dakon sonki a xuciyana sai gashi allah ya amshi adua ta ya mallakamin ke am so happy zara,haka da mukaje mukayo alola tareda yin slh kama kaina yayi yamin adua kafin ya miko ledan daya shigo da shi kazane tareda nonoh nasha sosai sannan ya mike ya fita mikewa nima nayi na yi wanka sannan nasa kayan bacci , nafara bacci naji mutun yana shafani mikewa nayi da shirin sa ihu kissin dinna ya farayi(ae ko ina gani haka ni neerat na fita a guje ko rufe masu kofa banyi ba dan ni yarinya ce kar naga abinda yafi karfina) . Bani na koma gidan ba sai bayan shekara3 xuwa nayi naga zarau da yara biyu suna xaune akan capet suna wasa, Fita nayi na je gidan umar ganin nayi naga fateema tareda yaro1 umar kuwa yana cin abinci. Stil barin gidan nayi naje gombe hauwa nagani da ciki tana zaune.
.
.
Allahamdulilah .kunga yarda karshe Zuwaira ta kare ita da Nuriyat dan ko hausawana cewa duk nisan jifa tabbas kasa xai dawo, haka ko indan xaka tuna ramin mugunta to ka tuna karami danko baka san ko na jini ka bane zai fada .
Na gode da kuka samu daman karanta littafin, ayau na xo karshe littafin BA BAIWA BACE
.
Sai mun hadu a wani littafin.
.
#Hausa Novel 📓
#IP
Title :
Ba Baiwa Bace Part 5 Final
Description : *** BA BAIWA BACE PART 5 *** ******* KARSHE ******* . Juyawa dan ganin suwaye Hassan ne ya shigo tareda iyayensu amma banda hajiya zuwair...
Rating :
5