Mubarak a zaune a gefen gado, Sadiya a tsaye a kansa tana zubar da hawaye.
“Mubarak ashe za ka iya tsana ta haka? Wanne bakin laifi na aikata maka za ka yanke mini wannan hukuncin? Ka shigo mini da Karuwa har gida kuna aikata tsinanniyar rayuwa.”
Ya dago kansa da sauri ya kalle ta
”Ki yi dai a hankali kar ki zage ni.”
”Ba na fatan zuwan wannan rana, amma hakan baya nuna cewa zan ki fadar abun da ke zuciyata, ka cuce ni Mubarak.”
Ya kalle ta ya girgiza kai a kufule
”Za ki tunzura ni fa.”
Ta kalle shi da mamaki
”Ka dade ba ka tunzura ba.”
Ya tashi a tsaye ya kwashe ta da mari, ya tsaya yana kallonta da huci, ta kalle shi da dafaffen kunci
”Ba zan lamunci haka ba, ga mari ga tsinka jaka. Na rantse in ka sake gwadawa, zan rama.”
Ya tunzura ya girgiza kai sa’an nan ya je ya kulle kofar dakin, ya dawo ya rufe ta da duka, ta fara kici-kicin kwatar kan ta, har zuwa lokacin da ta hango plate din lemon fata da wuka a gefe, Sadiya ta kwace ta nufi gurin ta dau wukar ta juyo ta burmawa Mubarak da ke biye da ita a makoshinsa, ya kwanta a kasa yana hargagi.
Ta yi kansa a firgice! Wa zai shaide ta ya nunawa duniya cewa bisa kuskure, a yanayi na kwatar kai ta kasha mijinta?
A cikin dimuwa a cikin wannan tunani da yanayi ta fito a gidan, da nufin neman mafaka kafin wayewar gari ta san abun yi, Sadiya ta fito, Sadiya tana gudu, tana sauri-sauri har zuwa lokacin da ta fito titi, kaddara ta hada ta Dan Hajiya kafin su rabu ta bar shi da Jidali
.
Wannan duk shudadden al’amari ne, sabon al’amarin shine ga Dan Hajiya ga ‘Yan Sanda biyu Mudi da Tanko sun sako shi a gaba da tambayar ya fada musu in da Abokiyar aika wannan mummunan aikin take, da suka matsa masa da tambaya shi kuma ya ce ya bar ta a hotel, suka sako shi a motarsu shiga ba biya suka bazamo. Suka shiga kowanne lungu da sako na hotel din ba ita, suka fito a fusace har zuwa jikin motar su, Mudi bayan ya tabbatar Dan Hajiya ya dauru sosai da ankwa, ya daga hannu ya kwada masa mari a fusace.
“Idan ka ci gaba da raina mana hankali, za ka ci bakar wahala, ya za ka ce mana a nan ka bar Yarinya, yanzu kuma mun zo ba ta nan.”
Dan Hajiya ya waigo ya kalle shi yana zubar da hawaye, ban a halin da ya tsinci kansa a ciki ba sai na mutuwar Mamansa , kuma a lokacin da ya kamata ya kusanci gawarta da hawaye, sai ga shi a cikin ankwa
“Ranka ya dade ni fa sawun barawo na taka, a hanya kawai na gan ta na taimaka mata na dauke ta.”
Mudi da Tanko suka yi murmushi.
”Da a ce ka yi wannan bayanin naka tun a daddare lokacin da muka kama ka, kila da zai amfane ka, amma yanzu duk abun da za ka fada kirkira ce kawai.”
Suka tura keyarsa cikin motar, a gefe wata tsohuwa ce a rakube tana rawar sanyi, bayan da motar ta tafi, ta dan yi nisa, mai shigar tsoffin ta kwaye fuskarta. Sadiya ce, magujiyar da ta falfala ta bar banza Dan Hajiya da Jidali, Makashiyar da a k enema ruwa a jallo!
.
Mafarar labarin!
Se kucigaba dabina danjin yadda abin yake ai dama shege se shege...
Barkanku da rana..."
Kasance da mu akodayaushe dan JOining din mu ko kuma
Title :
Azal Part 6
Description : Mubarak a zaune a gefen gado, Sadiya a tsaye a kansa tana zubar da hawaye. “Mubarak ashe za ka iya tsana ta haka? Wanne bakin laifi na a...
Rating :
5