Duk abubuwan da Mubarak yayi ta ambaton zai yi mata, sabanin hakan ne yake faruwa da ita bayan aurensu, ya yi ta shelanta ba ta farin ciki, ba ta ga komai ba sai bakin ciki, y ace zai kasance a gefenta yayin tsanani ko damuwa, amma Sadiya sabanin hakan ta riska.
A wani lokaci a irin lokutan da ba ta sanin yanayin da take ciki, Kawarta Hajara ta yi sallama ta shigo ba tare da Sadiya ta lura da shigowarta ba har zuwa lokacin da ta zo ta bugi kafadarta, ta dawo hayyacinta da murmushinta.
”Kawata sannu da zuwa, ban san kin shigo ba.”
Hajara ta yi murmushi sa’an nan ta samu guri ta zauna
”Ya za’a yi ki san na shigo bayan kina a wata duniyar daban da irin ta mu, mai ke damun ki?”
Sadiya ta ja numfashi
”Ke dai bari kawai, ni a yadda nake ji yanzu ma ba abun da baya damu na.”
.
”Ke kuwa mai zai dame ki, bayan kin yi auren ki da wanda kike so.”
Hajara ta fada tare da alamun mamaki. Sadiya ta yi murmushin karfin hali
”Wannan shine babban kuskuren da na aikata a rayuwata, auren wanda nake so da zuciya daya, son da ya makantar da ni na kasa ganin jabun son da yake mini.”
.
“Mai kike so ki ce Sadiya?”
.
“Ba sai nace ba, ta muguwar ramar da na yi ma kawai ya kamata ki gane cewa ba na cikin kwanciyar hankali, ta yaya kike tsammanin hankalina zai kwanta bayan mijina bai damu da al’amurana ba, bai damu da cin abincina ba, ga yawon dare, wani lokacin sai na yi barci na gaji bai dawo ba.”
Hajara ta girgiza kai tare da tausayin qawarta
”To ki kai maganar gaban manya mana.”
Sadiya ta tabe baki
”Bani da wannan damar, kuma ma ko akwai ina ganin yayi wuri na fara kai korafinsa tun yanzu.”
.
”Shikenan, sai ki ci gaba da zama a cikin duniyar damuwa, dama wucewa zan yi shine nace bari na shigo mu gaisa, zan koma.”
.
Hajara ta mike, Sadiya ta mata rakiya zuwa jikin kofa ta dawo ta zauna ta koma duniyar tunaninta, ba tunanin damuwarta ba, a wannan karon tunanin kuskuren da ta tafka a rayuwarta, kuskuren da ya faru a wani lokaci na kafin aurenta.
.
Babanta ya kira ta, ta zo ta durkusa a gabansa.
“Sadiya ita rayuwa har kullum gaba a ke hangowa, kar ki yi abun da za ki zo ki yi dana sani daga baya, aure abu ne da a ke son yin sa muddin rai.”
“I na son sa Abba.”
Ta dago kai ta kalle shi sa’an nan ta mayar da kan ta, shi kuma ya ci gaba da cewa
”Ba son da kike masa ne abu mai muhimmanci ba, abu mai muhimmancin shine shi wanne irin so yake miki?”
Suka yi shiru na wasu dakiku sa’an nan Baban ya ja gwauron numafashi ya kalle ta
”Shikenan ta shi ki je.”
Wannan shine zama na farko, ita da Babanta. A zama na biyu kuma, kiranta ya yi a fusace.
”Sadiya, ba da yawuna ba ‘yan uwan Mubarak sun zo mini da batun auren ki, ni nace ki turo su?”
Ta yi shiru, bayan wani lokaci ya gyada kai ya ci gaba
”Ban san cewa wuyanki yayi kwarin da kike tsammanin ke za ki yiwa kan ki aure ba, rashin son alakarki da Mubarak baya nufin cewa ba na son ki, hasali ma hakan shine kauna ta kololuwa da zan nuna miki, amma tunda tunaninki daban da irin wanda nake miki, ba komai, ki je , Allah ya bada zaman lafiya.”
Ta yi murmushi ta tashi da nufin barin gurin ya bi ta da kallo
”Yauwa dakata, bayan auren ki idan wani abu ya faru ko wata matsala ta fara bibiyar rayuwar , kar ki tuna damu.”
Wannan shine kuskuren Sadiya na Kafin aure Kafin riskar kanta a ranar bakin cikin da ya fi duk wani bakin cikin baya.
A ranar da Dadddare Sadiya tana kwance, bayan wani lokaci wayar Mubarak da ke ajiye a gefensa ta fara vubration, ya farka ya dauki wayar, ya tashi a zaune firgigit bayan ya ga sunan Cecelia, ya kuma kallon wayar sa’an nan ya kalli Sadiya. Ya daga kiran ya fara magana kasa-kasa
"Cecelia bisa wanne dalili za ki kira ni a wannan tsohon daren?"
.
"Eh kiranka na yi na fada maka ka fito ina jiranka a kofar gida. "
Ya zaro ido
.
" Ba na son wasa."
.
"Idan ka ji karar bugun kofar gidan, kila ka gaskata."
.
"Cecelia mai yasa ba kya son zaman lafiya ne?"
.
"Kai ne dai ba ka son zaman lafiya, idan kaddara ce ta hana ka aure ni, yanzu ma ita ce ta hana ka bani lokacinka? Ka fito ina jiranka, in ba haka ba za ka yi mamakin ganina a tsaye a kan ka "
Ya mike a tsaye firgigit.
" Haba dai Tawan, gani nan fitowa, kin dai san auren nan na yi shine kawai saboda an matsa mini a gida, kuma abun da ya hana na kai musu ke a matsayin zabina shine ba za su yarda ba. "
Ya fara shirin fita a dakin, yayin da Sadiya take barcinta.
.
FARFAJIYAR GIDAN MUBARAK
Mubarak yana tafiya zuwa dai-dai kofar gidan, ya bude. yana budewa Cecelia ta shigo, ya bi ta da kallon mamaki.
" Mu je. "
Ta ce
Ya kalle ta da tunanin ta zautu
" Mu je ina?"
.
"Cikin gidan mana, yau a nan zan kwana."
Ya girgiza kansa
"Ai girman ki ne ran ki ya dade."
Ya zagaya ta bayanta ya rufe gidan, ya juyo.
.
SADIYA BED ROOM
Sadiya a kwance, a cikin magagin barci ta fara laluben Mubarak a kan gadon, ta ji ba shi, ta farka a zaune tana waige-waige kafin daga baya ta tashi a zaune, ta zuro da kafarta kasa ta mike a tsaye sa’an nan ta fito zuwa parlour, ta shiga toilet ta duba ta tarad da baya nan, ta fito tana waige-waige ta zauna a kan kujera sa’an nan ta dafe kanta tare da damuwa, a lokacin ta hango takalmin mata a dai-dai kofar dakin Mubarak, ta razana sa’an nan ta ja baya a cikin halin rudani.
Ta bata rai sa’an nan ta ja dogon numfashi tare da girgiza kai ta tashi ta nufi jikin kofar a fusace, ta buga da karfi.
.
IDAKIN MUBARAK
Mubarak da Cecelia suka tashi a zaune firgigit a kan gadon a tsorace suna zazzare ido, suka kalli juna sa’an nan suka mayar da kallonsu kan kofar dakin. Mubarak ya waigo ya kalli Cecelia
.
"Cecelia, ya a ka yi ta san muna nan?"
Cecelia ta waigo suka hada ido
"Na mata yadda za ta gane hakan ne."
.
"Ban gane ba? "
.
" I na nufin da sani na bar takalmi a kofar dakin saboda in ta fito a dakinta ta san muna nan"
Kallon da yake mata ya koma na mamaki.
"Bisa wanne dalili?"
"Yadda na ki zaman aure na fusata na bankawa gidanmu wuta, zaman lafiyar duk wata mace a gidan aurenta shine abun da na tsana. "
Sadiya ta sake buga kogar da karfi, Mubarak ya sauko kasa ya goya hannunsa a bayansa yana kaiwa da komowa a gaban gadon, Cecelia tana kallonsa. Bayan wani dan lokaci ya dawo da kallonsa kan ta.
" Cecelia, ba mutum ba ce ke. "
" Tun ba yau ba ya kamata ka san da haka. "
Ya girgiza kai
" Da ban sani ba, amma yau din na sani, kuma daga yau din irin wannan ba zai sake faruwa ba."
Ko da hakan ba za ta faru ba, Mubarak bai san cewa ba zai sake numfashi ba.
"Ko bai faru ba, burina ya cika, na tabbata al’amarin nan ya isa ya sa aurenka ya samu tangarda."
Ya kalle ta ya girgiza kai a fusace, sa’an nan ya dawo da baya ya zauna a kan gadon.
.
BAYAN AWA DAYA
Sadiya ta gaji da bugawa ta dawo ta zauna ta yi tagumi, tana shesshekar kuka, a haka har barci barawo ya zo ya dauke ta.
Daga jikin kofar dakin Mubarak, ya bude kofar a hankali ya leko ya ga yanayin da Sadiya ta ke ciki sa'an nan ya koma cikin dakin, bayan wani lokaci Cecelia ta fito a dakin tana tafiya a hankali har ta je jikin kofar fita a falon, a dai-dai nan Sadiya ta farka, Cecelia ta waigo su ka hada ido
"Yadda kika hana ni zaman lafiya a gidan aurena, Allah ya hana ki jin dadin rayuwar nan."
Ta fada a fusace , Cecelia ta bude kofar ta fita da sauri.
Tafaru ta qare...
Abu Abdullah ke muku barka da safe..
Kasance da mu akodayaushe dan JOining din mu ko kuma
Like
https://mobile.facebook.com/%C3%9FADI-%C3%9FA-RAI-1468881616743257/
join
https://mobile.facebook.com/groups/102487536763796?view=group
like(y)ßADI ßA RAI
joinßADI ßA RAI..
and join our group
https://mobile.facebook.com/groups/461721127364011?view=group&refid=18
Title :
Azal Part 5
Description : Duk abubuwan da Mubarak yayi ta ambaton zai yi mata, sabanin hakan ne yake faruwa da ita bayan aurensu, ya yi ta shelanta ba ta farin c...
Rating :
5