Mubarak ya so ya ji kunyar karyar da ya sheqawa Sadiya saboda ba abun da ya faru ba kenan, a zahiri abun da ya faru shine shi da Abokansa Sunusi da Musa sun fito daga ciki zuwa farafajiya suna dariya, ya musu rakiya har zuwa jikin motarsu, suka bude suka shiga, sa’an nan Musa da yake bangaren da Mubarak yake a tsaye ya leko ta saman gila shin motar.
"Ina fatan daga wannan ranar za ka manta da Cecelia. "
Mubarak yayi murmushi
" kokarin da nake ta yi kenan, so nake a ce auren nan ya zame mini sanadiyyar barin munanan halaye, a qalla dai ace ko ban zama Limamin masallaci ba, na zama Ladan."
Suka bushe da dariya sa'an nan suka tada motar suka fita a dai dai lokacin da wayar Mubarak ta fara burari a aljihunsa, ya ciro ta ya tarad da Cecelia ce ke kira, ya yi murmushi sa’an nan ya daga kiran.
"Wuni daya da aurenka ka manta da wata halitta irina."
.
"Ashe zan iya mantawa da waye ni."
.
"Ba ka san halin da nake ciki ba ko? Baqin cikin za ka bata darenka da wata, ya sa na yi kuka kamar ba gobe."
.
"Kin dai san ba zan lamunci zubar hawayen ki ba, ki kwantar da hankalinki , ba zan iya barin ki ba, saboda ke din ta musamman ce, ki shirya ma a nan zan kwana kawai."
Ya kashe kiran, sa’an nan a ya kashe wayar gaba daya, amma ba waya da kira kawai ya kashe ba har da farin cikin Sadiya.
Ya dan tsaya na wasu dakiku sa’an nan ya waiga baya, ya nufi motarsa ya bude ya shiga ya tada ya fara tafiya, ba da mota ba kawai har da farin cikin Sadiya.
.
BAYAN KWANA 2
wa Sadiya za ta fadawa yanayin da take ciki, da ya za ta zauna ta tattauna matsalolin ta cewa kwanaki kadan bayan aurenta matsalolin aure suka fara bibiyar ta, cewa har yanzu Mijinta bai kusance ta ba?
Ta bar matsalolin ta tsakaninta da zuciyata, yanzu haka gata nan ta shiga kitchen ta girka abinci kala-kala, ga Sadiya nan ta zo kan dining table ta jere abincin, ga ta nan ta shiga bandaki ta yi wanka ta tsala kwalliya ta zo tana jiran Mubarak.
A wannan lokacin, Mubarak yana zaune a majalisin sheke ayarsu suna bushe bushe da kada karta abunsu
Musa ya kalle shi
"Ango, gaskiya ya kamata a ce ka tashi ka tafi gida yanzu, kana shiga hakkin yarinyar nan fa."
Mubarak ya harare shi
"Musa yaushe ka san ya kamata? Har ka fara fadarta, ni fa ko a ranar da kuka mini rakiyar ango, maganganunka na hankali sun bani mamaki, na dade ina tunanin an ya kai ne ma kuwa."
Sunusi ya bushe da dariya.
"Ban da abun ka Mubarak a wannan lokacin ai kowa ya san gaskiya, ita kuma ba a bukatar daga bakin wanda ta fito Kafin a karbe ta. "
Mubarak ya tabe baki
" Haka ne, amma dai ban shirya zuwa gida a yanzu ba, kai ni fa wani lokacin ma mantawa nake cewa ni ango ne."
Suka bi shi da kallon mamaki, Musa ya ja numfashi ya ce
"In dai Cecelia tana nan, ba abun mamaki ba ne in ka manta da kan ka ma."
Suka bushe da dariya
.
*
.
Sadiya tana ta jiran Mubarak har barci ya dauke ta. Mubarak ya shigo yana waige-waige har ya hangonta, ya tabe baki ya karasa wajenta.
"Sadiya, Sadiya."
Ta farka tana mutsittsike ido tare da magagin barci.
"Sannu da zuwa. "
Ya fadada murmushinsa.
" Yauwa, ya na gan ki a nan, in barci kike ji ki shiga daki ki kwanta mana."
Sadiya ta yi yaqe.
"I na jiran ka shigo ne ka ci abinci tukuna."
.
"Nan gaba ki bar jirana, sai da naci abinci a waje na shigo. "
Ta bata rai.
" Mubarak, wai wacce irin zamantakewa mu ke, wanne irin so kake mini? Kafin aurenmu kana zumudina, yanzu ba ka yi, da kana son farin cikina yanzu kuma damuwata ita ce muradinka, ina iyakar bakin kokarina don ganin cewa na kyautata maka, yayin da kai kuma a bangarenka abun ya kasance sabanin haka."
Yayi murmushi
"Idan kika ci gaba da korafi a kan halayyata, wacce abu ne mai wahala na chanza, za ki hadu da hauhawar jini a banza, mafi dacewa shine ki yi hakurin zama dani a yadda nake."
Hawaye ya gangarowa kan fuskarta
"Gaskiya wannan ba Mubarak din da na sani ba ne, Mubarak din da na sani ba haka yake ba, Mubarak dina ba ya son damuwata, ba ya son bacin raina, Mubarak dina mai yalwar murmushi ne, fuskarsa mai annuri ce... Mararraba ta farin ciki."
Ya bi ta da kallo
"Da a ce za ki komawa rubuta littafan soyayya, ba karamar tsada kalaman nan naki za su yi ba."
Ya tafi ya bar ta, ta ta bi shi da kallo sa’an nan ta fashe da kuka.
ALLAH dai ya sakama mata....
Abu Abdullah ne kemaku Barkan ku dadare.
Title :
Azal Part 4
Description : Mubarak ya so ya ji kunyar karyar da ya sheqawa Sadiya saboda ba abun da ya faru ba kenan, a zahiri abun da ya faru shine shi da Abokansa S...
Rating :
5