Dan Hajiya ya nufi gadon da Hajiyansa ta ke da sauri ya kama hannunta, sa’an nan ya fashe da kuka. Lokacin da a ka kira shi a ka sanar masa cewa lallai-lallai ya zo tana nemansa bai san cewa mutuwa za ta yi ba,
Likita ya bi gawar Hajiya da fuskar tausayawa sa’an nan ya dawo da kallonsa kan Banzan d’an ta
”Saboda tana son sanar da kai wani muhimmin al’amari ta so ta gan ka kafin mutuwarta, ashe ba ku da sauran rabon ganawa a duniya.”
Ya juya ya fita a dakin, ya bar Dan Hajiya da nadama da tunanin nasihar da ta yi ta masa a baya, ya tuno da wani lokaci day a bar ta ya tafi gidan Yarinyarsa Linda bai dawo ba sai bayan kwana biyu, kwana biyun da Hajiyansa ba ta runtse idonta ba da nufin barci ko gyangyadi. Ya shigo cikin falon ba tare da ya yi sallama ba, Hajiya ta bi shi da kallo cike da fushi ba tare da ya lura da ita ba, lokacin da ya lura da ita sai karasa gurinta da sauri ya durkusa.
”Hajiya ina kwana? Ai ban gan ki ba saboda tsabar barci da ya rufe mini idanu, hurhudu nake ganinki Hajiyata.”
Ta yi murmushi, amma na karfin hali ne kawai.
”Ai ba abun mamaki ba ne in ka ganni tara-tara ma.
”
Ya sunkui da kansa kasa
“Hajiya a masallaci fa nayi kwanaki biyun nan, kai Allah ya kara mana son Annabi.”
Ta yi busasshen murmushi.
”Dan nan Kaza tana take ‘ya’yanta ne ba don ba ta son su ba, saboda haka duk abun da zan fada maka gaskiya na ke fada maka, gyara kayanka ne.”
.
“Hajiya wallahi ina jin wadannan wa’azaozin naki, amma matsalar da a ke samu ita ce daga na fita a nan sai na neme su na rasa.”
Ta kuma yin murmushi
”Ni dai abun da nake so da kai shine ka bar duk wadannan ayyukan asshan da kake, shin za ka so a na aikata tsinanniyar rayuwa da ‘yar uwarka kamar yadda kai kake da na wasu, kuma ko ba don haka ba ma, ka duba fa kai ne babba a cikin ‘ya’yana, kai nake kallo, shin ba ka tunanin damuwar da nake ciki a duk lokacin da a ka zo mini da labarin ba dadi game da kai?”
.
“Tunanin da na kasa yi kenan har yau, mai yasa bana tunanin damuwarki Hajiya ta?”
Ya fara mikewa da niyyar barin wurin, ta bi shi da kallo
”Allah ya shirye ka.”
”Ameen sama-sama, Hajiyata.”
.
Damuwar da bai yi tunaninta ba har zuwa fitar numfashinta na karshe! Duk duniya ita kadai ce ta damu das hi, ‘yan uwa da sauran dangi sun yi banza da shi saboda bakin halinsa, yanzu rayuwa ta zame masa ba shi da kowa kenan!
Ya dawo a tunaninsa da ganin ‘yan sanda biyu Mudi da Tanko sun cuso masa bindiga a ka , daya yana kokarin sa hannunsa a cikin ankwa.
“You are under arrest!”
Ya juyo ya kalle su da fuskar kuka.
”Ranka ya dade da alama dimuwa kuka yi, ku bar ni na ji da abun da yake damuna.”
Tanko ya yi murmushi
”A na zarginka da laifin kisan kai, barinka a kowanne irin yanayi shine babbar katobarar aikinmu na shekara goma sha tara.”
Dan Hajiya ya zaburaa
”Ranka ya dade ni ko kiyashi ban taba kashewa ba.”
Mudi ya mayar masa da cewa
”Saboda ba ka da matsala da shi ne, kana bata mana lokaci.”
Zai karasa in da yake ya sa masa hand-corp ya ci gaba da cewa
”Mu je ka nuna mana in da ka boye abokiyar aikin naka.”
.
”Ranka ya dade wallahi kaina ya kulle bana gane komai, ku mini hakurin duk wani abu sai bayan na gama yiwa gawar Mahaifiyata gata sa’an nan in yankan naman jikina ma za ku yi a shirye nake.”
Tanko ha Harare shi
“Idan ba ka mata gata ba a halin rayuwa, kila ma bakin cikin halin ka ne yayi sanadiyyar bugawar zuciyarta, wanne gata kuma za ka mata bayan ranta?”
Za su tasa keyarsa a cikin waigen kallon gawar Hajiyarsa, ba kukan kewa da rabuwa da ita kawai yake ba, har da na sabuwar rayuwar da ke shirin kusantarsa, abun bakin cikin shine zai dau tsawon lokaci na rashin haduwa da yarinyarsa Linda!
Shin wa zai warware wannan al’amarin? Wace ce Sadiya, bakar bakuwar da ya marabta, ta gudu ta bar shi da Jidali? A ina zai ganta ya kalli tsabar idonta ya ce da ita “Kin cuce ni. "
Wace ce Sadiya? Bakuwar da Dan Hajiya ya marabta , ita kuma ta gudu ta bar shi da Jidali.
Rayuwarta ta kafin aure sassauka ce, ta bayan aure c eta zo ma ta sabanin zato, ta zo ma ta da rudani da jumurda.
Ranar da take farin ciki, ranar cikar muradinta, Jama’a suka yi tururuwa a kofar gidansu a ka daura aurenta, Sadiya tana farin ciki ta samu Mubarak.
Da daddare a ka kai ta gidan Mijinta, Sadiya tan a farin ciki ga ta a gidan Mubarak da lullubabbiyar fuska tana jiran Abokansa su kawo ma ta shi, Sadiya tana so tag a farin cikin da ya ke cewa zai nuna mata, Sadiya tana ta zumudin zuwan Mubarak.
.
09:37 PM
Ango da Abokansa biyu Sunusi da Musa suka shigo gidan, suna hira da dararraku.
”Ango ka sha kamshi.”
Musa y ace das hi, yayi da Mubarak yake gyara babbar rigarsa yana murmushi
”Kar ka so ka ga yadda nake zumudin zuwan wannan ranar,amma ban san mai ya faru ba daga shigowa ta gidan nan, na nemi walwala ta ba rasa.”
Sunusi ya tabe baki
”Ya kake fadar ka nemi walwalarka ka rasa da fuskar murmushi?”
Suka tsaya suna kallon juna suna murmushi.
”Ka dai san ba zan fada da fuskar kuka ba, koma dai yaya ne abun da nake so na fada muku shine, na tsinci kaina a wani yanayi da bana farin ciki.”
.
SADIYA BED ROOM-
Sadiya a zaune a gefen gado a cikin kayan amarci, fuskarta lullube da mayafinta , Mubarak da Abokansa sua shigo bayan , Kowa ya nemi gurin zama in ban da Mubarak da ya zauna a kusa da ita.
Musa da Sunusi suka kalli juna sa’an nan suka yi murmushi.
“Da alama za mu sha bakar wahala kafin bakin amaryar nan ya sayu. Kila Haka ne ya sa Kawayenta suka gudu suka bar mu daga mu sai ita saboda mu yi ta fama.”
Cewar Sunusi, yayin da Musa ya ce
“Kila dai kai kadai kake ganin wahalar, amma ni bana hango komai sai saukin kan ta, da saukin halinta.”
Mubarak ya kalle ta ya dawo da hankalinsa kan su
ya ce
”Batunka shine gaskiya Musa.”
Sunusi ya tabe baki
“Ni kuma nawa karya ko?”
Suka fashe da dariya gaba daya
”To dai shikenan, shawarar mu gare ku ba ta wuce wacce kuka saba ji ba, ku qi ku qi gani, kuma ku mayar da komai ba komai ba, ku zauna da juna cikin hakuri da girmamawa, wadannan sune gishirin zamantakewa.”
Abokan Mubarak suna ta yi musu nasiha, har zuwa tsawon lokacin da suka mike da shirin tafiya, Sunusi ya ce
”Kai, da alama zumudin ganin amaryar nan ba zai bar ka ka mana rakiya ba.”
Mubarak ya yi murmushi
”Ban da abun ka, ko ba domin rakiya ba, ai zan je na rufe kofar gidana.”
Suka yi sallama da Amarya, Mubarak ya biyo bayansu, Amarya Sadiya tana ta babbaka dariyaa a cikin mayafinta, tana ta ganin kamar rike lokacin a ke a duniyar zumudinta, tana so Mubarak ya yi sauri ya je ya rufe kofa ya dawo gare ta… Sadiya tana ta zumudin ganin farin cikin da ya yi ta ambaton zai ba ta yayin hira da zamantakewar soyayyarsu.
Sai dai abun da Sadiya ba ta sani ba shine Angonta ba zai dawo gare ta ba a wannan lokacin, yana kan hanyar zuwa gidan yarinyarsa Cecelia.
KARFE DAYA NA DARE
DAKIN SADIYA
.
Abun da Sadiya ba ta yi zato ba shine ya faru da ita, farin cikinta ya fara kokarin zama bakin ciki, angonta daga kawai ya bi Abokansa za su tafi shi kuma ya rufe kofa, tsawon awanni bai dawo ba. Ta kwaye gyalenta tare da damuwa, ta zuro kafafuwanta kasa sa’an nan ta mike a tsaye.
“Wannan wanne irin al’amari ne, daga kawai ya ce zai je rufe kofa har yanzu shiru kamar an aiki bawa garinsu.”
Ta fito ta duba, Angonta baya falo, baya kitchen, baya toilet, baya farfajiyar gida , ina ya tafi? Tambayar da kuka ya mata rakiyar laluben amsarta.
.
04:OOam
DAKIN CECELIA
.
Mubarak a kwance yayin da Cecelia ke gefensa, ya tashi a zaune a firgigit ya kai kallonsa kan agogo, bayan nazarta sai ya zuro da kafafuwansa kasa, ya mike ya nufi in da agogo da hularsa suke, dai-dai lokacin da shedaniya Cecelia ta farka. Ta kalle shi tana mutsittsike ido
“Ba dai tafiya za ka yi ba.
”Ai na ma yi kokari, wanne ango ne zai iya irin wannan rashin adalchin a darensa na farko, Allah sarki baiwar Allah yanzu haka tana can cikin zulumi.”
Ya fada ba tare da ya kalle ta ba, ya fara daura agogonsa sa’an nan ya waigo ya ce da ita
”Sai haduwa ta gaba.”
Ta yamutsa fuska.
”Kai, Namiji mugu ne, har yanzu mamakin dalilin da ya sa baka aure ni ba nake.”
.
”Wannan kuma batu ne na qaddara.”
.
“Kaddara ko son zuciya?”
Yayi murmushi kawai.
“Ni kin ga na tafi, sai a lokaci na gaba.”
.
06:50am
DAKIN SADIYA
Sadiya ta kasa zaune ko tsaye, tun tana kuka hart a tsinci kan ta a lokacin da kukan ya ki zuwa, a wannan karon ma da ta dauko wayarta ta gwada kiran lambar Mubarak , amsar daya ce da sauran kiran baya “The number u dial is switch off.” Ta yi jifa da wayar, a Dai dai lokacin da Mubarak ya turo kofar dakin ya shigo, ta daga kanta da sauri ta kalle shi, shi ma ya bi ta da kallo tare da sanyin jiki. Da sauri ta je ta zube a gabansa tana kuka
”Haba Mubarak, wanne irin abu ne wannan? Ashe ba za ka so kwanciyar hankalina ba, ashe za ka iya mayar mini da farin cikina zuwa baqin ciki, ashe za ka iya mayar mini da dariyata kuka, ashe za ka iya mayar da kwanciyar hankalina zuwa tashin hankali, ashe za ka iya mayar mini da daren da nake alfahari da shi zuwa daren da ba na marari, ashe za ka iya mayar mini da gadon aurena makara, a wannan lokacin ban dace na amshi hukunci da kukan baqin ciki ba.”
Ta kuma fashewa da kuka
”Da za ki saurari uzurina da ba ki yanke mini hukuci da bahaguwar fahimta ba.”
“Ba wani uzuri ko dalilin da zai sa ka qi kusantata a daren farkonmu, sai dai ko in dama ba muradinka ba kenan.”
“Kin dai san rai sama yake da komai, to bayan fitar mu sai Abokina Sunusi ya yanke jiki ya fadi. Na san ko ke ce kika tsinci kan ki a irin wannan yanayin abun da za ki yi bai wuce ki kai shi asibiti ba.”
A zahiri a wajen Mubarak ba ceton rai ne sama da komai ba face bukatarsa!
Namiji rigar qaya... Adaibi ahankali...