ALBARKA HOTEL
ROOM NO:- 19
Sadiya, bakuwar Dan Hajiya a zaune a gefen gado tare da damuwa tana kallon TV, damuwarta ta juye zuwa dimuwa bayan ganin sanarwar cigiyarta da photonta tare da zargin dabawa mijinta wuka a makoshi da kuma shelanta ganinta da jami’an tsaro suka yi da Dan Hajiya.
Sadiya ta dawo cikin hayyacinta tare da jan dogon numfashi, sa’an nan ta tashi da sauri ta dauki gyalenta ta fita a cikin dakin bayan ta yi bad da kama zuwa wata tsohuwa da babu yadda za’a yi kuma ba zai yiwu a gane ta da sauki ba.
Tana fita a dakin, shi kuma Dan Hajiya ya fito a cikin toilet da gejeren wando kawai a jikinsa yana goge ruwan kansa da towel, ya tsaya das akin baki galala bayan ya fahimci Sadiya bata nan, ya dan fara waige-waige kafin daga baya ya basar tare da watsa hannu sama.
”Tafiyarta ta fi nono fari, na ci moriyarta ba ta da wani amfani a wajena yanzu, bari na gaggauta zuwa asibitin nan amsa kiran Hajiya ta.”
Bai san cewa Sadiya ta gudu ta bar shi da jarfa ba !
Ya jefar da towel din sa’an nan ya fara shirin sa kayansa.
.
11:05
HOSPITAL VERRANDER
Sargeant Tanko da Mudi suna tafiya a kan Verrander, har zuwa dai-dai ofis din Likita, suna shirin turawa shi kuma ya fito, suka ka gaisa.
“Likita akwai wata marar lafiya mai suna Hajiya Saude Abdullahi. ’
Tanko y a ce a shi.
Ba tare da dogon nazari ba, shi kuma mayar masa a takaice cewa
“Eh akwai.”
Tanko ya girgiza kai
“Waye yake zaman jinyarta?”
Likita ya girgiza kai tare da tausayi
“Allah Sarki, matar abun tausayi, tun jiya ta damu da sai ta ga danta, shi kuma bai damu da al’amarinta ba, a karshe ma kashe wayar ya yi.”
Mudi ya yi murmushin gamsuwa
“Dole ba zai zo ba, amma abun da nake so na sanar da kai shine ya shigo cikin wadanda a ke zargi da kisa, mun je gida nemansa amma ba mu samu komai ba sai wani mutum da ya sanar mana yanayin da lafiyar Hajiyansa ke ciki.”
Likita ya zaro ido tare da mamaki.
Mudi ya tabbatar masa da
“Kwarai kuwa, saboda a daren da al’amarin ya faru ya yi mana basaja da matar marigayin a matsayin matarsa.”
Likita ya ce
“Ta ina kuke so na ba ku gudunmawata?”
Suka yi musayar Lamba, da cewa da zarar ya ji motsin Dan Hajiya ya sanar musu.
.
HOSPITAL PACKING AREA
Dan Hajiya ya yi packing din motarsa ya fito ya hau kan verrander asibitin, a can a gabansa yana iya hango Seargent Mudi da Tanko sun rabu da Likita sun juya baya suna tafiya, ya bi su da murmushi , yana murmushi ba tare da ya sna abun da zai faru da shi a gaba ba!
“Shegu ‘ya’yan wahala, a asibitin ma sai sun yi cuta.”
Ya ci gaba da tafiyarsa , yayin da Hajiyarsa ke a kwance a kan gado, numfashinta yana fita sama-sama, ta fara magana da hardaddiyar murya.
“A.. Nemo min dana kafin na mutu, ina so mu yi magana.”
Numfashinta ya ci gaba da fita sama-sama, a dai-dai nan Likita ya turo kofa ya shigo, Dan Hajiya yana biye da shi, a dai-dai wannan lokacin ne kuma Hajiya ta yi kalmatush-shahada ta cika!
Ba ta da sauran rabon ganin baqin ciki!
A gefe guda Nafisa ce a gefen Hotel a cikin bad da kama, yayin da gari ya cika da photunan nemanta, Mutane suna ta tattauna dalilin da yasa ta kasha mijinta duk kuwa da cewa auren soyayya suka yi, soyayyar ma ta gani kasha ni? Wa zai iya ba su amsa?
I ta dai ta buya, ta bar Dan Hajiya da jarfa!
Maganin dan banxa kenan...aigobe ya qara.."
Ilalliqa'a ya ikhwanee...
Title :
Azal Part 2
Description : ALBARKA HOTEL ROOM NO:- 19 Sadiya, bakuwar Dan Hajiya a zaune a gefen gado tare da damuwa tana kallon TV, damuwarta ta juye zuwa dimuwa b...
Rating :
5