(labarin alhaki kwuikuyo)
.
NA Abubakar AUYO
.
Qarfe
04:05PM
KOFAR GIDANSU HAJARA
.
"Dan Hajiya wai ya maganar aurenmu ne?"
"Magana tana nan daram, sai dai..."
Hajara ta katse shi a fusace
"Sai dai me?"
Ya tabe baki
"Kawuna da zai zo gidanku a yi maganar auren yayi accident a hanyar cotonou, an ma yi sa’a da ya farfado da ransa da karaya uku, yanzu makomar soyayyar mu tana hannun warakarsa. "
Ta kalle shi a raine
" Haba sabon dan duniya, kar ka raina mini wayau mana, ni zaka mayar wawiya."
Ya kalle ta sa'an nan ya zaro sigari a Aljihunsa ya banka ma ta wuta.
"Ba mayar ki zan yi ba, dama ai ita ce. In ban da daqiqin tunani wacce mace ce namiji zai neme ta yayi fasiqanci da ita sa’an nan ta yarda zai aure ta? Kafin ni wa ya san da adadin mutanen da kika yi, kuma bayan aurenmu wa ya san da wadanda za ki yi? Kuskure ne da ki ka yarda muka dora maganar mu a kan aure bayan fasiqanci, kin ga duk iskancin nan da nake da ilimina, tar nake ganinki, gwara ma ki yi hakuri dani in ba haka ba in janyo miki hau, in janyo miki jarfa."
Jikin Hajara yayi sanyi, yayin da shi kuma ya koma da baya da karfin jiki ya shiga maoarsa. Ya tada ta, ya nufo gurin Hajara.
"Bani guri na wuce, ko na taka ki, kuma na taka banza."
Ta bi motar da kallo har yayi nisa, sa’an nan ta ja dogon numfashi da fuskar nadama.
.
11:15PM
GIDAN LINDA
Burarin da wayarsa ta ke, shi ya tashe shi a nannauyan barcin da ya dauke shi, tare da magagi ya fara laluben wayar har hannunsa ya tabo ta, ba tare da lura ba Dan Hajiya ya daga kiran.
"Na gaji da fada maka cewa abun da ba zan lamunta ba a cikin munanan halayenka shine yawon dare."
Ya tashi a zaune tare da karamar razana bayan ya ji muryar Hajiyansa. Ya mayar mata da
"Hajiya, da a ce kin san ba yawon banza nake ba, da kin kwantar da hankalinki kin yi barci."
Yana iya jiyo sautin murmushin karfin halinta ta cikin waya.
"Haba dan nan, in dai ba kaddara ce ta juyo maka da babin shiriya ba, ban ga alamar za ka taba yin wani aiki da ba na banza ba. "
Ya waiga gefensa ya kalli yadda yarinyarsa Linda ta sau baki tana sharara barci, sa'an nan ya dawo da kallonsa kasan gadon, ba komai sai filtar sigari cunkus da kwalbar syrup.
" Hajiya ki bar duk wani shakku, a yanzu haka ina babban masallachi ban da hailala da salatin annabi ba abun da nake yi.
"Mutumen da dimuwa take sa ya manta da in da gabas take, babban abun mamaki ne in ya zo da labari irin naka, kai ba ma abun mamaki ba kawai, tatsuniya ce, maza ka hanzarta ka bar duk in da kake yanzu ka dawo gida, in kuma ba haka ba zan gwada maka mummunan bacin raina."
Ya katse wayar a fusace sa’an nan ya waiga inda Linda take. Babu yadda za'a yi ya iya barin ta a wannan lokacin ko da kuwa hakan yana nufin zuciyar Hajiyansa za ta buga Buuum!
.
03:11am
TITI
Dan Hajiya shi kadai ba a cikin matarsa ba kawai har a titin yana jin kida yana busa sigari, har zuwa lokacin da ya hango wata Mace a cikin hargitsattsen yanayi a gefen titi tana tsayar da shi, har ya zo dai -dai in da take ya wuce sai kuma ya tsaya ya dawo da baya da tunanin yadda take doguwar nan ko da Fatalwa ce, wannan wata dama ce da bai kamata ya bari ta wuce shi ba
.
"Malam ka taimaka mini, ina cikin..."
Ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu
"Haba baiwar Allah, in ban da dai neman ki batawa Malamai suna, ta ina na yi kama da Malamai, ko a cikin 'yan iska qarshe ne ni, a gidan caca kuma kartagi ne, sallamammen Babana ne ni na Kafin mutuwarsa. "
.
" Ni dai koma yaya ne ka taimaka mini, tsayawa jan dogon bayani zai iya bani matsala."
.
"Yanzu mafaka kike so na baki ko wajen kwana? "
.
" Ni duk wanda ya samu ina so."
.
"Zan taimake ki saboda kawai mace ce ke, ba zan rasa ta in da zan fanshe wahalata a gare ki ba, shigo mu je."
.
Ya bude mata, ta shiga, Ya ja suka tafi, sai dai abun da Banza Dan Hajiya bai sani ba shine Amarya ce ta kashe mijinta ta gudu, shi kuma yake shirin ba ta mafaka.
Da ya sani bai saurare ta ba, bai san za ta zame masa sanadin da rayuwa za ta zo masa a wani yanayi irin na ba gaba ba baya ba.
Da sannu zan ci gaba da saka muku zaren labarin!
Title :
Azal Part 1
Description : (labarin alhaki kwuikuyo) . NA Abubakar AUYO . Qarfe 04:05PM KOFAR GIDANSU HAJARA . "Dan Hajiya wai ya maganar aurenmu ne?...
Rating :
5