Kungiyoyi da wasu manazarta kan rubutun harshen Hausa ne suka halarci taron daga kasashen da suka hada da Ghana da Nijar da kuma jihohin tarayyar Najeriya.
Mallam Ado Ahmed Gidan Dabino na daga cikin mutanen da suka shirya taron, yace mahalartan sun tattauna tare da samo mafita dangane da wasu kalubale dake ciwa marubuta litattafan Hausa tuwo a kwarya, musammam ma a yankin nahiyar Afirka ta yamma.
Batun kiyaye ka’idojin rubutu wajen wallafa littattafan Hausa, na daga cikin batutuwan da aka tattauna a taron. A cewar farfesa Bello Salim na jami’ar Bayero ta Kano, shine yawancin mutanen da aka koyawa ka’aidodjin rubutun Hausa basa aiki da shi.
Taron dai ya amince cewa yakamata dukkannin mawallafa da marubuta littattafan Hausa, su kiyaye da batutuwan da aka cimma a matsayin hanyoyin warware kalubalen da aka gano suna mayar da hannun agogo baya ga sha’anin bunkasa harshen Hausa.
Title :
Anyi Taron Marubuta Litattafan Hausa A Kano
Description : Kungiy oyi da wasu manazarta kan rubutun harshen Hausa ne suka halarci taron daga kasashen da suka hada da Ghana da Nijar da kuma jihohin t...
Rating :
5