Kotu ta yanke hukunci akan shugauban kasar Afirika ta kudu akan kudaden daya dauka ya gayara gidan shi.
Ana zargin Jacob Zuma, shugaban kasar Afirika ta kudu da yin watsi da kundin tsarin mulkin kasar inda ya dauki kudaden jama’a yayi amfani dasu ya gayara gidan shi.
Shugaban masu shari’a na kasar, Mogoeng Magoeng, a kotun tsarin mulki dake Johannesburg ya bayyana cewa ” Zuma ya kasa wajen tsare kundin tsarin mulkin kasar a matsayin shi na mafificin doka a kasar.
Wannan hukuncin yazo ne bayan da Zuma ya gama fuskantar zargi cewa wani dangin wasu mutnae yan asalin Indiya sun taka rawa wajen nade naden Ministocin da yayi.
Tun hawan shugaba Zuma tattalin arzikin kasar Afirika ta kudu ke yin kasa. Amma saboda farin jinin jam’iyyar shi, da kuma rinjaye da take dashi a majalisar kasar, da wuya a iya cire shi daga shugabancin kasar.
” Shugaban kasa Zuma dole ya biya da kanshi kudaden da baitil malin kasa yace ya biya. Maganganun da akeyi na gyara tsaron gidan shi ko a 2014 Dala Miliyan 24 ne kawai, akan Dala Miliyan 214 daya amsa.
Thuli Monsela ya bayyana cewa, shugaba Zuma ya amfana da wannan aikin na nkandla a yankin Kwalu-Natal.
Shugaban kasa Zuma tun farko yaki amincewa da cewa yayi almundahana inda ya sanya kwamitocin bincike, wanda daga bayan shugaban yan sanda ya bayyana cewa wajen wanka na waje da akayi anyi shine domin hana gobara.
Jam’iyyun adawa zasuyi amfani da wannan damar da aka samu domin su samu nasarori a zaben kananan hukumomi dake tafe a kasar. Taya daga cikin bakaken kasar sun rasa aiyukan su nayi.
Zuwa 2019 ne shugaba Zuma ke cika wa’adin karewar mulkin shi karo na 2. Wanda daga nan ba zaya iya tsayawa ba a bisa tsarin mulkin kasar.
Idan za’a iya tunawa, shugaba Zuma yazo Najeriya a wannan watan inda suka tattauna da shugabaBuhari kuma yayi jawabi a majalisa.
Title :
Ana Sharrin Tsige Shugaba Kasar Afirka Ta Kudu
Description : Kotu ta yanke hukunci akan shugauban kasar Afirika ta kudu akan kudaden daya dauka ya gayara gidan shi. Ana zargin Jacob Zuma, shugaban kas...
Rating :
5