Musayar wuta ta barke tsakanin dakarun sojojin Nijeriya da 'yan Boko Haram a wani gari da ake kira Bita, wanda ke kusa da garin Gwoza a jihar Borno.
Artabun wanda aka fara shi tun a daren jiya a yayin da 'yan bindigan suka yi yunkurin kwace garin Gwoza, sun afkawa sojojin ne a daidai garin Bita bayan sun yi kicibus da su, inda har zuwa safiyar yau ana kan musayar wutar, kamar yadda majiyarmu ta Daily Trust ta rawaito.
Majiyar ta ce har sai da dakarun sojojin suka yo odar jirgin yaki daga garin Yola domin tallafawa dakarun sojojin na kasa, wanda zuwan jirgin ya taimakawa sojojin.
Garin Gwoza dai na daga cikin garuruwan da Sojoji suka kwato daga wurin 'yan Boko Haram a jihar Borno, inda har wasu daga cikin 'yan yankin da suka yi gudun hijira sun dawo gidajensu.
Title :
Ana Musayar Wuta Tsakanin Sojoji Da 'Yan Boko Haram A Jihar Borno
Description : Musayar wuta ta barke tsakanin dakarun sojojin Nijeriya da 'yan Boko Haram a wani gari da ake kira Bita, wanda ke kusa da garin Gwoza a...
Rating :
5