A jihar Bauchi ‘yan jam’iyyar APC mai mulki sun zargi gwamnatin jihar da karbar na Goro akan kwangilar kwaskwarimar hanyar cikin garin Bauchi, da kuma kwangilar sake fasalin gidajen matan gwamnan jihar.
A lokacin da yake hira da manema labarai, wani jigo a jam’iyyar ta APC mai suna Alhaji Abdulwahab Gambu, yace sun gwammace jiya I yau, domin ma’aikata da masu karbar fansho baki daya har yanzu suna shan wuya, sai gashi an fitar da makurden kudade ana gyaran gidajen matan gwamnan jihar.
Babban mai tallafawa gwamnan jihar Bauchi a fannin labarai da mu’amula da jama’a, Kwamarad Sani Mohammed, ya mayar da martani kan wannan zargi inda yake cewa aiki na gudana yadda ya kamata, ya kuma bayyana batun karbar na Goro a matsayin yarfin siyasa ne kawai.
Bayan da wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Mohammed ya yiwa Kwamarad Sani tambayar sa cewa, an saba ganin manya manyan kamfanoni na irin wannan aiki na Biliyoyin Naira, amma sai gashi ana ganin jama’a dauke da diga da wilbaro suna yin wannan aiki. Kwamarad ya bayar da amsa da cewa, “mutanen da kaga suna kananan ayyuka ana yi ne domin tsarin APC ne domin ganin duk abinda aka kawo jiha, an sami yan jihar Bauchi suna amfana.”
Sai dai kuma a halin da ake ciki a kwai yiwuwar daukaka kara kan batun karbar bashi da gwamnatin jihar Bauchi ta yi na Naira Miliyan Dubu 400 daga bankin UBA.
Sources VOA Hausa
Title :
An Zargi Gwamnatin Jihar Bauchi Da Karbar Na Goro Kafin Ya Bayar Da Kwangila
Description : A jihar Bauchi ‘yan jam’iyyar APC mai mulki sun zargi gwamnatin jihar da karbar na Goro akan kwangilar kwaskwarimar hanyar cikin garin Bauch...
Rating :
5