Rundunar sojojin Nijeriya tace an samu gawar hafsan sojin ta da aka sace a karshen mako, Kanar Samaila Inusa yau Talata da misalin karfe 6 na yamma.
Sanarwar da rundunar sojan ta bayar ta hannun Daraktan yada labaran ta Kanar Sani Usman Kukasheka tace ana kyautata zaton an kashe hafsan ne ranar da aka sace shi, domin har gawar ta sa ta fara lalacewa.
Rundunar ta ce an samu gawar ce kusa da kauyen Ajyaita dake wajen Kaduna.
Daraktan ya bayyana cewar rundunar sojin ba za ta yi kasa a gwuiwa wajen zakulo wadanda suka kashe hafsan dan hukunta su ba.
Title :
An Kashe Hafsan Sojan Da Aka Sace
Description : Rundunar sojojin Nijeriya tace an samu gawar hafsan sojin ta da aka sace a karshen mako, Kanar Samaila Inusa yau Talata da misalin karfe 6 n...
Rating :
5