Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa kawo yanzu ta gano ma'aikatan bogi fiye da dubu ashirin da biyu a cikin tsarin albashi na jihar.
Ciki kuwa har da kananan yara 'yan shekaru takwas zuwa goma da aka gano sunayensu a matsayin malaman makarantu.
Gwamnatin dai ta yi ikirarin cewa yayin bankado ma'aikatan na boge, an gano wasu sunaye na karya, yayin da wasu kuma ma'aikata ne da ke karbar albashi fiye da sau daya, kana akwai wadanda suka yi ritaya daga aikin gwamnati amma suna ci gaba da karbar albashi.
Wani kwamiti da gwamnatin jihar ta kafa domin tantance ma'aikatan gwamnati, da malaman makarantu, da kuma 'yan fansho a matakin jiha da na kananan hukumomi ne, ya bankado cuwa-cuwar.
Mai taimaka wa gwamnan jihar ta Bauchi kan harkokin watsa labarai, Comrade Sabo Muhammad, wanda kuma ke daya daga cikin jami'an sadarwa na kwamitin, ya yi wa wakilinmu Ishaq Khalid karin bayani.
Title :
An Gano Ma'aikatan Bogi Dubu 22 A Jihar Bauchi
Description : Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa kawo yanzu ta gano ma'aikatan bogi fiye da dubu ashirin da biyu a cikin tsarin albashi na jihar....
Rating :
5