Yarinya 'yar shekaru sha biyu mai suna Zulaihat Adam da RARIYA ta sanar da bacewarta a ranar Talatar da ta gabata a garin Mararrabar Abuja da jihar Nassarawa, an gano iyayenta bayan kwanaki uku da bacewarta.
Bayan sanar sa bacewar yarinyar da RARIYA ta yi, jama'a daga ciki da wajen kasar nan, sun yi ta kira don su san halin da ake ciki gama da bacewar da yarinyar ta yi. Inda kuma a dalilin sanarwar ne aka gano gidansu yarinyar.
Ita dai Zulaihat an kawo ta aikin gida ne daga unguwar Tudun Wada dake jihar Kaduna, zuwa garin Mararrabar Abuja da jihar Nassarawa, inda bayan azabtar da ita da uwardakin ta take yi ne a tsawon watanni kusan biyar da ta ti tana aikin gidan, sai ta gudu ta bar gidan, wanda kuma a sakamakon kullen da ake yi mata a gidan sai ta kasa gane ko'ina, har ta kai ga ta bata.
Mutumin da ya yi ta dawainiyar Zulaihat har aka gano iyayenta, Malam Buhari Yunusa Kumurya, ya bayyana cewa bayan sun tsinci yarinyar ne sai suka mika ta ofishin hukumar kare hakkin mata (WRAPA) dake Abuja, inda a nan ne iyayenta suka zo suka karbe ta. Sannan kuma hukumar ta ja wa iyayen yarinyar kunne don gudun kada hakan ya sake faruwa a nan gaba.
Babbar sakatariyar hukumar ta WRAPA, Hajiya Saudatu Mahdi, a yayin jin ta bakinta game da lamarin, ta ja kunnen iyaye mata da su kasance masu kishin 'ya'yansu musamman mata, tare da kauracewa mika 'ya'yansu ga aikin gida.
Yar mahaifiyar yarinyar, wadda ake yi wa lakabi da Maman Nafi, ta nuna nadamarta kan bada yarinyar da suka yi a matsayin 'yar aiki, inda suka bayyana hakan a matsayin lalura.
A gefe daya kuma binciken da RARIYA ta yi, ta gano cewa a yayin da hukumar ta WRAPA ta yi tattaki har sau biyu zuwa gidan matar da yarinyar take yi mata aiki, ta gudu ta bar gida.
A yayin da wakilinmu ya isa gidansu Zulaihat dake Tudun Wada, Kaduna, ya tarar da ita cikin fara'a, bayan ta koma cikin 'yan uwanta. Zualaihat ga ce ba ta fatan ta sake tsintar kanta cikin mawuyacin halin da tsinci kanta a ciki, wato aikin gida. Ta kara da cewa burinta a yanzu shine Allah ya hore wa mahaifiyarta kudin da za ta sanya ita da kanenta a makaranta.
*Hoton Zulaihat tare da wakilin RARIYA, Aliyu Ahmad a yayin da ya yi tattaki zuwa gidansu Zulaihat a Kaduna a yau Asabar.
Title :
An Gano Iyayen Yarinyar Da Ta Bace A Tsakanin Kaduna Da Abuja
Description : Yarinya 'yar shekaru sha biyu mai suna Zulaihat Adam da RARIYA ta sanar da bacewarta a ranar Talatar da ta gabata a garin Mararrabar Ab...
Rating :
5