Daga Umar Bandi Kofar Kware
Jihar Sakkwato tsohuwar cibiyar Daular Musulunci wadda ta yi suna da fice a fagen daukaka addimin Musulunci, a dalilin jihadin Shehu Danfodiyo, a fagen siyasar mulkin dimokuradiyya ta yi wa sauran jihohin kasar nan nisa a dalilin Sir Ahmad Bello Sardaunan Sakkwato wanda masu mulkin yau ke famar yin kira akan a yi koyi da nagartattun halayensa na kamanta gaskiya da adilci, wanda a cikin sa ne yarasa ransa dana iyalansa hadi da makaraban gwamnatinsa.
Ginuwar inuwar rayuwar jima’ar a karkashin inuwar Daular Musulunci ya gina musu katafaren tauhidi hadi da tausayi da tausayawa da yin halinjinkai da tallafawa marasa galihu, zamani ko gurbacewar al’amurran da kudi ko son kudi ke ginawa, wasu daga cikin ‘yan kasuwa na fakewa da tashin Dala ko Saifa sun kara hauhawar farashin kaya, ta kai suna cika shagunan ajiyar kaya da daga kasa har sama, a tsakanin shinkafa da Shuga, da zimar cin kazamar ribi a dai-dai wata mafi daraja da daukaka a wajen Allahwatan azumin Ramalana.
Lamarin bai tsaya ga kayan da kamfanoni keyi, har shinkafar da muke nomawa a cikin kasa wadda ake kira Bahausa ta sami nata karin, wadda ake saidawa kamin zuwan haka, naira dari uku yau ta samuwa ne akan Naira dari hudu kwano, wadda ake sai dawa akan dari hudu da ashirin ta koma Naira dari biyar, wani abin mamaki su kansu masu sayarda ruwan leda Table water, sun tada farashi daga Naira hamsin jikar ruwa mai dauke da kwaya ashirin ana saidawa mai daya naira biyar, su kansu sun tada farashin zuwa Naira dari ko wace, kudin da kayan jika biyu ta koma daya.
Wani abin haushi da takaici, ba haka lamarin yake a jihar Zamfara da jihar Kebbi, wadanda dukkaninsu har zuwa jihar Naije a cikin Sakkwaton aka fitar dasu, amma basa tsalawa kaya kudi suce da mai saye farashin dala ya haura, irin wannan rashin tausayi da neman tara abin duniya idanu rufe duk mai wahala basu da wata damuwa, yana daga cikin abubuwan da wasu ke zargin cewa shi ne ya janyo yawan tashin Gobara a kasuwanninmu, da wuta ke biyar lungu da sakon kasuwa ta lakume komi tabar masu bakin buri da mugun nufi rafke da hannuwa, lamari abin dubawa ne akan rashin tausayi da tausayawa da ‘yan kasuwar mu kuma musulmi masu fatar in sun mutu su sadu da rahamar Allah da zai kaisu shiga Aljanna, amma sun cire tausayi da tausayawa al’umma idan suka mutu a cikin wannan hali mai zasu shedawa Allah gobe.
Kara farshin kaya da ruwan ledar, daga naira biyar zuwa goma, ya zama dalilin da masu wannan sana’a masu neman abin sawa bakin salati, kulla ruwa a fararen ledoji suna sai dawa jama’a naira biyar, wanda yin haka ya zama abin dori ya dawo muna a jihar Sakkwato wanda ana fatar gwamnatin jihar Sakkwato zata zauna da masu gidajen yin rowan laida, domin taji dalilinsu na lunka kudin ruwa dag naira hamsin zuwa dari, shinko abin da suka kira Karin farashin kudin leda na iya zama gaskiya in har ya zama gaskiya yana iy zama da dilin kara naira hamsin?
Masu fashin bakin siyasar jihar, suna zargin yin halin ko inkular gwamnatin jihar akan barinsu suna yin yadda suke so na daya daga cikin abubuwan da suka janyo Karin tsadar rayuwa a jihar, lamarin da ake jin ko wace shkara musamman lokacin azumin watan Ramalana, ‘yan kasuwa a jihar suna tsalawa kayan su kudi, lamarin dake Karin samar da bala’oin fitinu da yawan tashi gobara, da take iya shafuwar wanda bai san hawa bale sauka, sau da yawa ake samun wani mutum ya yanke farashin kaya kamar Shinkafa, ko Shuga domin sawakawa jama’a amma wasu na zargin ‘yan kasuwar da rabawa kananan yara kudade suje su saye kai ji irin wannan halin in ya tabbata ba tausayi da tausayawa ga mai yinsa.
Title :
An Dawo Da Ruwan Sha Na Dauri A Jihar Sokoto
Description : Daga Umar Bandi Kofar Kware Jihar Sakkwato tsohuwar cibiyar Daular Musulunci wadda ta yi suna da fice a fagen daukaka addimin Musulunci, a...
Rating :
5