Kotu ta yankewa tsohon dan wasan Sunderland, Adam Johnson, hukuncin zaman yari na shekara shida kan samunsa da laifin lalata da 'yar shekara 15.A lokacin da yake yanke masa hukuncin alkali Jonathan Rose, ya ce dan wasan ya ci amana, ya kuma haddasa bacin rai ga yarinyar da ya ci zarafinta.
Kotun ta ce Johnson mai shekara 28, ya ci gaba da yin lalata da yarinyar duk da ya san cewa shekararta 16 da haihuwa.
Sai dai kuma kotun ta ce dan wasan ya daukaka kara kan hukuncin da aka yanke masa.
Johnson ya fara taka leda a Middlesbrough daga nan ya koma Manchester City ya kuma je Sunderland a shekarar 2012, ya buga wa Ingila wasanni 12.
Sources BBC Hausa
Title :
An Daure Adam Johnson Shekara Shida
Description : Kotu ta yankewa tsohon dan wasan Sunderland, Adam Johnson, hukuncin zaman yari na shekara shida kan samunsa da laifin lala ta da ...
Rating :
5