Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya bayyana cewa yadda ake gudanar da zabuka karkashin mulkin Buhari na nuna cewa Buharin kawai yafi gane a rinka zubar da jinin mutane maimakon zaben gaskiya da za a kare cikin salama da adalci.
Fayose yace irin kashe-kashen da aka yi a Bayelsa irinsu aka maimaita a Rivers saboda Buhari ya manta Allah ke bayar da mulki ba tashin hankali ba.
Fayose ya kara da cewa irin jinin bayin Allah da aka zubar saboda Bukatar son kai yasa na ce Allah yayi fushi, kuma da Buhari Allah ke fushi.
Fayose yace dama tun a shekarar 2015 yayi hasashen wannan yanayi da rashin kwarewar Buhari zai jefa kasar nan to ga shi abu ya tabbata saboda haka Buhari ya jirayi fushin Allah inji Fayose.
Fayose yace hatta taron warware matsalar tattalin arziki da Buhari ya kira a Abuja wannan taron babu wani abu da zai tsinana domin Buhari ya shiga fushin Allah a cewar Fayose
Title :
Allah Yana Fushi Da Buhari - Fayose
Description : Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya bayyana cewa yadda ake gudanar da zabuka karkashin mulkin Buhari na nuna cewa Buharin kawai yafi gane ...
Rating :
5