Bisa ga dukkan alamu YM Bello ya shaqa, duk da cewa wasu lokutan maza ba su cika damuwa ba wai don 'yammatansu sun ambato wasu samari na daban, matuqar ba maganar wata tsohuwar soyayya suka yi ba, galibi 'yammatan ne ba sa qaunar su ji samarinsu suna hirar wata mace a gabansu, ko da kuwa akwai alaqa tsakanin samarin na su da su ko babu, abin mamaki MB Bello dai ya yi saurin hawa a nan, wannan ya sa Mari ta fara qoqarin arcewa ta bar su, don ta fara tunanin wargajewar zancen dan nan gaba kadan, irin maganganun da Jummai ta yi hatta Mari duk da rashin kan-gadonta ta ga shirmenta, duk wani namiji da za a yi masa haka dole ya nuna bacin ransa in dai ba soyayyar ce ta yi daga-daga da zuciyarsa ba.
.
Yanzu dai ba ta da wani zabi da ya wuce ta ba su wuri su sulhunta kansu, nan take ta figo Jummai gefe guda "Don Allah YM minti Biyu, lokacin tafiyata gida ya matso" ta saukar da murya qasa-qasa "Ke me kike yi haka Jummai? Irin wannan sai ki bata alaqarki da hannunki, maza fa wani lokaci kamar sigari mai zobe ne, ba a cika gane kansu sosai ba, dan wannan abin da kike rainawa yana iya yin amfani da shi ya bata abin da ke tsakaninku, kin ga ke za ki yi nadama, mutum kamar wannan in aka same shi lallaba shi ake yi ba riqon sakainar kashi ba, da haka kika bata alaqoqinki na baya, ki qirga zuwa yanzu samarinki nawa?" Jummai ta fara ba ta amsa da qarfi, Mari ta katse ta "Sh-sh-sh! Ba terere na ce ki yi min ba, in ina so ya ji ne don me zan jawo ki nan wurin?"
.
Tana rufe baki ta waiwaya ta ga YM a jingine da mota yana dan kada qafa kansa yana kallon wani wuri, tabbas bai san halin da suke ciki ba, qawancen Jummai da Mari akwai matuqar ban mamaki, don in Jumman ta rako Mari haka suke rabuwa ba fahimtar juna, tana ganin cewa Mari tana tura wa namiji jiki sosai, wanda hakan zai iya kai ta ga asarar budurcinta ba tare da ta sani ba, ita kuwa Mari gani take yi Jummai na wasa da damar da Allah ya ba ta, irin haka ne ya sake maimaituwa ko a yau dinnan.
.
Maganar da Mari ta yi ba ta yi mata dadi ba, sai ma cewa ta yi "Ba sai na gaya miki yawan samarina ba, kin san su duka, ni duk saurayin da ba zai kai kansa gaban uwayena ba, to wallahi na san manufarsa, ba zan taba ba shi qofa ba, samarinnan da kike gani da yawansu ba su da imani, mutum zai nuna miki wata hanya da kansa, amma da wasu za su ba shi shawarar ya aure ki shi ne na farkon cewa ke 'yar iska ce, kuma in mutum da gaske yake yi me zai sa ya yi aiki da qaramin qwaqwalwarki ya cutar da ke sannan ya ce miki yana qaunarki? Wallahi YM Bello ya san abin da nake nufi sosai, matuqar ya yi kuskuren zama da mahaifana to bai da ikon zamewa, don za su sami mahaifansa su yi magana gemu da gemu"
.
Mari ba ta qara tanka mata ba, kallonta kawai take yi tana zuba, "In kika ga saurayi yana zullewa ba ya son wani abu ya hada shi da uwayenki wallahi macuci ne, gamawa da ke zai yi ya gudu, haka mamanmu ta gaya min, kuma ni kaina tun ban gane ba ga shi ya fara bayyana a sarari, shi ya sa duk wani motsi nawa ban yarda na yi face mamanmu ta san abin da nake ciki, don in an so cutata ma za ta iya taimaka min, duk samarin da kike cewa na yi ai na shaho ne, da na yi sake da tuni sun yi min sakiyar da ba ruwa, ba ki ga mu ma in ba ma son mutum ba ma yarda ya je wajen mahaifanmu ba?"
.
Daga nan sai Mari ta dan bugi bakinta ta ce "Ke ba ruwa na, ku qarata can, ni ban shirya jin wani wa'azi yanzu ba, kin ga tafiyata, ki ce masa sai wata rana in da rabon Allah ya kuma hada mu nan gaba, amma wadannan maganganun naki ba na tsammanin za su iya kai ki tudun na tsira, in ma ba ki qaunarsa ne ai gwara ki fito kawai ki gaya masa, in ta-so sai ku yi rabuwar mutunci, amma mutum a gabansa kina nuna masa qauna ta qarshe, ke ce fari da kwarkwasa, in kika ba shi baya ki nuna kamar ba ki san Allah ya yi ruwan tsirarsa ba, wannan ai yaudara ne ma zalla"
.
Ko waiwayowa ta kalli YM Bello ba ta yi ba, nan take ta hauri takalmanta ta ba kare sa'a, Jummai kuwa ta dawo wajen saurayinta ta iske shi yana dan shaqan qamshi kadan, duk da cewa ita ma Mari ta dagula mata nata ran, amma sai ta hadiye, ta shirya shiga wata jarabawar "Na ga alama maganar da na yi ne ta Baban Manar take damunka, mutumin da bai san abin da ake ciki a nan ba, kai in ka gan sa ma aka ce zai zama rival dinka ko kula maganar ba za ka yi ba, shi ma ta kansa yake yi, a cikin malamai ba a maganarsa don ba wani ilimi ne da shi ba, in kudi ne wanda zai jawo hankalin mace sai dai a yi maganarka, shi fa a sanina bai da wani katamaiman aiki bare ya ja da kai, to meye na damun kanka? Ba Baban Manar ba ko Baban Muntada ne me ya sha min kai da shi?
.
In ka bibiya YM bai damu da maganar wani Baban Manar ba, tunaninsa kawai yadda zai kawar da zancen tafiya wurin uwayen Jummai, a yanzu dai bai da wani makamin yaqar wannan maganar sai dai ya riqe wuta, ya nuna lallai kishi yake yi, don haka ya yi bakam yana jin ta "In kuma wannan waqar ta baqanta maka rai to ka yi haquri, in da na san hakan za ta faru da ban rera ba, Allah ne sheda, na qi kai ne ka matsa sai da na rera ta, ga shi kuma ta zama mana matsala" dukansu su Biyu babu mai buqatar wannan hirar ta yi tsawo, YM dai yana neman hanyar arcewa ne, ita kuma Jummai ban da halin da ta gan sa a ciki, ga Mari kuma ta ba ta haushi.
.
Ko da yake tana zaton cewa YM Bello ya damu ne, shi kuwa qoqarinsa kawai ta ga bacin ransa, albashi a qarshe ta yi qoqarin ba shi haquri, in ta so a janye wadannan maganganun guda Biyu masu alaqa da juna, har zuwa yanzu dai bai da wani shiri na zuwa qofar gidansu don zance, to bare kuma ya yi qoqarin ganin mahaifanta, wata qila zancen Jummai yana nema ya fito sarari kenan, abin da yake qoqarin yi yanzu ya nuna mata bacin ransa har ta ce ta janye maganganun, albashi in ta so a sake dago su wani lokacin nan gaba "Waye kuma Gali da Galiya?" In jishi "Kana da lokacin saurarata? Don labarin yana da dan tsawo kuma ba za ka fahimce shi ba sai a qarshe, sau da yawa irin wadannan labarurrukan na gaskiya suna qumshe da wasu darussa da koyarwa, amma gaskiya ba kowa yake fahimtarsu ba in ba wayayyun mutane masu ilimi irinku ba, masamman kai ma da kake da sha'awar literature na san za ka ji dadin labarin sosai"
.
Ko ba a fada ba YM Bello ya ji dadin kalaman Jummai na qarshe, don kuwa ta zugo shi, sannan ko ba komai za ta iya kama kanta da kanta matuqar zancen rayuwa da soyayya za ta yi, wanda shi ne manufarsa, a qarshe kuma tattauna labarin tana iya mantar da su zancen canja wurin hira, dama abin da yake so kenan, yana buqatar a tashi daga wurin ne ba tare da sun tsai da magana Daya ba, har dai ya samu ya yi tunanin yadda zai fito mata nan gaba "Ina sauraronki, kin san kuwa akwaini da son jin labari ko Qoje ma albarka, ba don ba ni da lokaci ba ai da Duniyar Marubutannan ta facebook sun sha mamaki" Jumai ta yi murmushi, dazu-dazunnan ya gama cewa bai da Hausa, kuma ma ba ta dame shi ba, asalin rigimarsu kenan.