.
"Ka yi qoqari, ai ba duka masu kudi suke yin abubuwa da kansu ba" in ji Jummai daga nan ta duqar da kai qasa ba ta sake cewa komai ba, ganin haka YM Bello ya dan damu, har ya tambaye ta, ita kuma ta ce masa ba komai, amma da ya matsa mata da tambaya sai ta ce "Ka san tun haduwarmu da kai har yau dinnan ba mu tattauna wani abu mai mahimmanci ba, alhali akwai wasu abubuwa masu matuqar mahimmancin gaske da nake so mu dan tattauna da kai domin dauwamar wannan soyayyar da ganin dorewarta, to amma ban san ta yadda zan fito musu ba, ina so ne na yi maka bayani filla-filla cikin 'yan kalmomi qalilan ba masu yawa ba"
.
YM Bello bai san irin tambayar da za a yi masa ba, ko tun farko ya nuna ba ya son tattaunawa kan maganar aure, ya ce soyayyarsu jaririya ce a bar ta ta dan girma tukun, da yake yanzu ta matsa tana son yin magana sai ya ce "Ki daure ki taqaita, sannan ban da karin magana, kin san ban fahimtar sarqaqqiyar magana, gwara dai Turanci, don in kin cire yawan zuwa qasashen Turai da mutum yake yi, galibin maganata duk da Turancin ne" "Tabdijan" inji Mari "Ashe Larabci ma har da na zubarwa kenan, ko ba ka zuwa qasashen Larabawa ne?"
.
To da yake YM Bello bai da haske ta wannan bangaren, kuma yana da tabbacin cewa galibin 'yammata suna suna yawan zuwa Islamiyya sai ya ce "Ina dai da yara masu zuwa qasashen Larabawa, ni ban cika zuwa ba, don yanzu duniya ta rikice gaba daya, in ka cika yawan zuwa wadannan qasashen yanzu sai a zarge ka da ta'addanci, ko a ce kana sufurin makamai, so Turanci kawai, ko ba komai mutum zai samu zama lafiya" Maganar ta so ta ba wa Mari mamaki, wato dai akwai yuwuwar ko zama a qasar ba zai yi ba nan gaba.
.
Jummai kuwa kallonsa ta yi da gefan ido ta yi wani dan murmushi mai daukan rai ta ce "Allah ya jiqan Baban Manar ba don ya mutu ba, wallahi kullum na tuna waqarsa ta Hausa sai na ji qaunar harshen ta dada kurdawa cikin zuciyata, na ji ba harshen da yake da hikima da fasaha kamar Hausa, shi ba Larabci ba ne amma yana qumshe da wasu abubuwa wadan da ba in da za ka same su sai a cikinta, akwai mawaqa da yawa a wannan qasar tamu, kamar su Aliyu Namangi Zaria, Aliyu Aqilu, Mudi Sipaka, Yusuf Aliy Tudun Maliki da sauransu"
.
Mari ta fara zungurinta da gwiwar hannu, tana nufin ta yi shuru, sai dai rashin sa'ar da aka yi YM Bello ya riga ya gani, sai ya tsaya kai da fata sai Jummai ta rera masa waqar, ita kuma ta qi, nan fa ya bata rai "To wa ma ya sani ko alaqar da take tsakaninku ta wuce ta waqa da jin dadinta? Ni ba ma wannan ba, shin waqar kike bege ko mai waqar?" Mari ta kalle ta da gefen ido kan cewa ta waske, to amma Jummai ba ta gani ba, ba ta ma gano cewa YM fa kishi yake ba, don haka ba wani abin da ya dame ta bare ta yi maganar ba shi haquri, tunaninta kawai ba ta iya rera waqa ba.
.
Ta dan juyo ta kalle shi "Idan na rera maka za ka ga kamar da kai nake yi, kuma wallahi literature ce kawai, ka san ni Hausa na karanta" YM ya girgiza kai "No! No!! Kwantar da hankalinki my dear, ni ban da wannan dabi'ar, sau nawa ina halartar Poets' Conference a Wales ta UK? Ba ki da mafita, sai kin karanto min waqar Baban Manar a kan Hausa don ban gama gamsuwa da abin da ta qumsa ba" Jummai ta sunkuyar da kai ta fara rerewa:-
.
"Gali da Galiya ku zan dora fadinta
Hausa a ko'ina ka je za ka ishe ta
Bar su American da Chech har su Jakarta
Ba bu qasar da za ka ce ba a fadinta
Sai ko mai fadinta ne ba a kulawa.
.
Rana ta fito duhu sai ya kwaranye
Kai mai gardaman hakan dole ka janye
Ko banza Sule Biyar ya dara ganye
In ka hada da sannu za mu yi rinjaye
Ruwa da wuta ku san da dai ba a hadawa.
.
Hausa a ko'ina na je ke na fi qauna
Don kin zarce harsuna kab a wurina
Dan maraqina ya fi garke na wanina
Dan kowa a ko'ina bai wuce dana
Haka harshen gari da dai bai wuce nawa.
.
Ya qi gida ku ce da shi "ka zama wawa"
Sai qauna kake ka zam dan Turawa
Ka bar salsalarka ma ba ka tunawa
Kai kullum fadi kake ban komawa
Ko an kai ni tabbatar ban zaunawa.
.
Hausa uwa, uba wurin masu fadinta
Kalmomin cikinta duk masu nagarta
Kai da jiyota za ka san babu irinta
Ni zan so ka zam cikin masu iyata
Ko an tashi hargitsi ba ka macewa."
.
"Iyakanta kenan?" In jishi, ta girgiza kai "A'a da saura, na dai karanto maka dalilin da ya sa nake qaunar waqan ne, don gaskiya yana da kyau mutum ya san martabar harshensa, kuma ya iya, tun da shi ya haife shi kuma har abada ba zai sami kamarsa ba" Mari dai ba ta iya cewa komai ba, don a ganinta bai dace Jummai ta karanto wadannan baitocin ba matuqar tana son alaqarta ta yi qarfi sosai da YM Bello, masamman yadda ta ga kamar ransa ya dan baci, Mari ta gama karantar YM sosai, shi Nigeriar gaba daya ba ta yi masa ba, to bare kuma wata Hausa.
.
"YM ka san maganar da nake so mu yi kuwa?" Inji Jummai, ya kamata a ce ta sami lokacin da ya fi wannan dacewa, to amma rashin kula bai bar ta ba, shi dai ya ba ta amsa da cewa "No!" Ta ce "Ina so ne mu dan juya wannan zancen ya koma wurin da ya fi dacewa, don wallahi ana min fada a gida, wai don me nake barin qofar gidammu zuwa wani wuri, sannan na zauna da wani saurayi? Ko last week ma da kazo sai da mamanmu ta ce na gaya maka tana son ta gan ka don ku tattauna wasu abubuwa masu matuqar mahimmanci wadan da suka shafi alaqarmu, kawai na kasa gaya maka ne"
.
YM ya dan yi murmushi "Da ni da Baban Manar din zamu tafi ko ni daya?" Mari da Jummai suka hada ido kowa ta bude baki, a lokacin ne ma Jummai ta fara gano cewa ta fa yi subutar baki, a daidai wannan gabar lamarin ya kasu mata zuwa gida biyu, shin za ta tsaya ba shi haquri ne, ko za ta share ne ta koma maganar ganawarsa da mahaifanta? YM zai iya yin amfani da wannan damar wajen kawar da batun da ake ciki, ita kuma Jummai babu wata alamar wasa a tare da ita.