Azkar din safe shine abinda Shaitan ba yaso kayi.. Yafi sanya Maka kasala da nauyin jiki da kuma barci mai nauyi adaidai lokacin da kake zaune zakayi Azkar din..
Ko kasan dalili??
Dalili shine gabatar da azkar din safe in sha Allahu zaisa ka samu damar Wuni cikin Walwala da annashuwa tare da samun kariya daga Sharrin Shaitanun fili da na boye.
Shi kuma shaitan yafi so ya ganka kullum acikin matsala! Shi yasa ba zaiso ka rika yin Azkar din ba..
Watarana Allah ya taimakeni na Kama wani Shaitanin Aljani Ajikin wani Saurayin Bil Adama. Sai na tambayi shi Aljanin :
ZF: Bismillahi wa ke tare damu?
ALJANI : Ni bani da suna.
ZF : To Musulmi ne kai, ko kafiri?.
ALJANI : Ni Musulmi ne.
ZF: To Kaji tsoron Allah ka gaya mun gaskiya. Shine menene ya kawoka jikin wannan yaron?
ALJANI : Na shiga jikinsa ne kawai don Mugunta. Ni nafi so in ganshi ko yaushe acikin matsala. Shi yasa na hanashi karatun addini ko na boko. Yana University ma amma ba ya fahimtar karatun.
ZF : Shin menene yayi maka, wanda har ya chanchanta kayi masa wannan muguntar? Shin ba ka tunanin gamuwarka da Allah ne?.
ALJANI : Ni babu Abinda nafi Qinsa kamar Azkar din safe. Idan yana yinsa, ji nakeyi kamar in kasheshi.. Da zai dena yin wannan Azkar din safen da tuntuni na hallakar dashi ma!!
Daga nan nayi masa Wa'azi amma bai yarda ba. Don haka muka ci gaba da Azabtar dashi har yasha wahala sosai. Daga karshe ya dauki Alkawari ya bar jikin yaron. Yanzu haka yaron ya koma yana ci gaba da Karatunsa.
Dukkan yabo da Godiya da iyawa sun tabbata ga Allah.
Shima Azkar din yamma yana da Muhimmanci kamar yadda na safen yake dashi. Don haka 'Yan uwa mu yawaita Zikirin Allah bayan Azkar din. Domin babu abinda yake Kusanta mutum zuwa ga Allah, kuma ya nesantar dashi daga sharrin Shaitan fiye ds Zikirin Allah.
Masu yawaita Zikirin Allah sune mafiya Qololuwar daraja acikin jerin darajojin Al'ummah. (KAMAR YADDA ALQUR'ANI YA FADA).
Wannan nasiha ce daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP. Da fatan Allah shi amfanemu da abinda muka karanta.
Pls idan bakayi Azkar dinka na safe ba, samu waje ka zauna kayi. Lojaci bai Qure ba.
Title :
Aljanu Basu Son Azkar Din Safe
Description : Azkar din safe shine abinda Shaitan ba yaso kayi.. Yafi sanya Maka kasala da nauyin jiki da kuma barci mai nauyi adaidai lokacin da kake zau...
Rating :
5