**** AL'AJABI PART 19 ****
.
A maimakon na iya cika umarnin da daddy ke bani sai na tsaya ina binshi da kallo kawai, idan na dubeshi sai kuma na juya na dubi faruk dake tsaye ya kasa cewa komai na tbbtr kunnuwansa a bude suke yaji abnd zan iya yi. Alkawarin dana daukarwa kaina na kasancewa da faruk a duk yanayin da yake ciki yasa duk wani tsoro yakau daga zcyta, ni ban wuce na tafi kmr yadda daddy ke cewa ba kuma bance komai ba har sai daya kara buga min tsawa a karona biyu. “Ki wuce mu tafi nace“. Maganar ta daki kwakwalwata, yaune karon farko da daddy ke daka min tsawa kai tsaye haka amma maimakon na firgita sai na kara gyara tsayuwa ma na tsaya kyam nace “daddy! ka dubi grmn Allah da manzonsa karkayiwa faruk haka, ka 2na sanda ya taimakemu ya rufa maka asiri kai kanka dani daduk danginmu, me yasa yanzu mu kuma ba zamu saka masa ba?? Idan wai don ni kakeyi don ka samar min da farin ciki ka rabani da wahala, to ka barni kawai sbd ni farin cikina anan gdn yake, faruk mijina ne har gobe kuma zan iya zama dashi a kowanne yanayi.“
.
Daddy ya zaromin ido yace “gsky na yarda baki da hankali, banda haukanki ina ke ina zama da nakasashshe makaho?? Abin kunyane ma ace kmr ni y‘ata mijinta makaho ne, abnd yayi mana a baya ya wuce mu gaba muke hange idan ke baki da 2nani mu muna dashi kuma bazamu bari wahala ta kasheki a banza ba, ki wuce nace!!“ Fuskata ta canja ma2ka naja da baya nace “Ina me baka hakurin cewa wlh ba inda zanje ba yadda za‘ai na tafi nabar gdn mijina wanda yaso ni sanda kowa ya gujeni yake kyamatata, kuma ba akan wani dalili ba.“ Cikin tsananin AL‘AJABI daddy ya bini da kallo yace “Ni kike gayawa haka??“ Ba tare da tsoro ba nace “Kayi hakuri amma ya zama dole in fadi hakan sbd kokoluwar butulci ne abnd kake so kuma banyi halacci ba idan nayi haka, na zabi na zauna anan har mu2wa tazo ta riskeni.“ Kin zabi wannan makahon akan mu iyayenki?? Daddy ya fada yana me nuno ni. Na gyada kai nace “Eh! haka nake nufi sbd mijina ne ko a wajen Allah hakkinsa a yanzu yafi naku. Hakanan dady yajuya yatafi tare da gargadin bani basu.
.
********************
faruk ne xaune abakin gado yana tatunanin dani kaina bansan me yake tunawaba.. Gyaran murya yayi alamun yanason yace wani abu naisaurin dago dakaina..yace HUMAIRAH.!! Nace na'am yace kishirya gobe zamuje gidanku."! Yinme? natan bayeshi..zamuje muba dady haquri akan abin daya faru.. Da SAFE WAJEN KARFE 10;00 ranar asabr..... Tsawon min2na talatin muka dauka sannan muka gama shirye-shiryen tafiya, abinda ya bani mamaki yadda faruk keyi tamkar zamu inda ba zamu dawo ba. Bayan mun gama kuma yace na rufe duk wasu kofofin gidan na ko‘ina, cikin rashin fahimta nace “wai faruk ina zamu ne?? Ina tsammanin cewa kayi gdnmu zamu mu dawo?? Meye kuma na sai mun garkame kofofi?? Faruk yadan hade fuska yace “ba gdnku zamu ba siyar dake zanje inyi.“ Duk da yanayin da nake ciki sai da nayi dariya na kada kai tare da cewa “Ba haka nake nufi ba faruk abin ne kawai ke bani mamaki,“Na dan taka daga gbnsa izuwa kan kujerar da hijabina yake, na kara yin dariya a karona biyu nace “wai ka siyar dani, ashema zaka iya siyar da kanka kenan??“ Naja sandarsa muka wuce kai tsaye izuwa waje tare da cgb da hira har muka fito izuwa harabar gdn muka zarce izuwa inda motar faruk take, na budewa faruk kofar ya shiga na mayar na rufe tare da zagayawa na shiga na tuka motar muka tafi.
.
Ckn nishadi muke tafiya ina sanar dashi duk wani wuri da muka gifta ko wani abu daya faru dai-dai sanda zamu gifta, a haka har muka iso tsaleliyar katafariyar unguwar, SARAUNIYA STREET!! makeken Allon dake kafe yayi mana maraba. 2n daga nan fuskata ta fara canjawa shekara daya curr kenan rabona da mahaifata na fara tuno rayuwar data faru dani a baya, na fara 2no lokutan baya sanda a wannan hanyar ake tukani a tsaleliyar mota, sanda nake takama ina fankama, nake ji da kaina. Ba yanzu da rayuwa ta canja ni ta karfin tsiya ba. A hankali muka cgb da ratsa kyawawan gine-ginen dake hamshakiyar unguwar da duk wanda ka gani a cknta to ya wuce raini, har muka iso tsalelen gdn namu. hmm... birki naci kawai a gbn gidan ina kallonsa, da ace wani zaizo wucewa yaga motar danake cknta da yadda na koma idan zanyi rantsuwa nan gdnmu ne bazai yarda ba. A hankali na danna worn har sau uku a hankali karamar kofar ta bude me bude gate din yabi motarmu da wani wulakantaccen kallo naji sanda kasa-kasa yake cewa “Bafa kowanne talaka ke shiga gdn nan ba.“ Waye ne?? Ya tambaya. Na sauke glass din motar a hnkl na leko da kaina waje, 2n kafin nace komai yaja da baya adan tsorace ‘ranki ya dade!!‘ Ya juya da sauri ya koma, jim kadan tafkeken gate din ya fara budewa. Naja motar izuwa harabar gdn nayi parking tare da fitowa ina me bin harabar gdn da kll sashe zuwa sashe. Abubuwa da yawa suka fara dawo min, duk inda na kalla sai wani abu ya fado min wanda faru a dai-dai wajen. Idona ya ciko da kwalla. Dai-dai lkcn ne faruk ya fito daga ckn motar wanda hakan ya dawo da hankalina gareshi na tako naja sandarsa muka nufi ckn gdn. Ma‘aikatan gdn kuwa sunyi dandazo sai gaisheni suke duk wanda na gifta ta kusa dashi, wasu ma harna fara manta sunansu. Da sallamarmu muka shigo tafkeken kayataccen falon, ba kowa sai hafsa y‘ar aiki tsaye a gbn plasma dake kafe tana y‘an goge-goge. Ta amsa sllmr tare da juyowa muna hada ido ta dafe kirji, LAH! aunty humaira!.
.
Hajiya! Hajiya!! Ga humaira tazo. Da sauri momi tare da daddy suka fito, momi ta dubeta tace “meye??“ hafsa tayi nuni damu. Dukkansu sukai turus suna kllnmu, momi ta dubi hafsa tace “To na gansu jeki.“ Hafsa ta ajiye duster dake hannunta ta juya tare dan dago min hannu tana murmushi, na gyada mata kai kawai ta fice. Daddy wanda ya kllmu ya dauke kai yaci gaba da gyara maballin rigarsa lkc guda ya dago kai ckn tsawa yace “uban me kuka zo yimin a gd?? Meya kawo ku??“ Na dan kara matsawa gaf da faruk nace “ka fada masa abnd kace kazo ka sanar masa kawai mu tafi.“ Faruk ya gyara tsayuwa yace “Zuwa nayi don na sanar dakai abnd nasan dole sai kayi dariya, abnd nasan shi kake so kaji kuma shi kake so ya faru. Insha-Allahu daga yau ka daina tsanata kuma komai yazo karshe.“ Faruk yaja hannuna izuwa kan kujera muka zauna. Momi da daddy ma suka zauna kunnuwanmu duk a bude so muke kawai muji me faruk zai fada. faruk yace “Alhaji na sani duk duniya ba wanda kake so kamar y‘arka guda daya wato humaira, sannan kuma ba wanda ka tsana kmr ni faruk sbd dalilai da yawa, musamman yanzu da dalili me karfi ya karu akan nada. Banga laifinka ba don kana son kwatowa y‘arka yanci donta rayu ckn rayuwa me dadi da nayi 2nani ma sai naga hakika kafini gsky. Nayi iya nazarin da zanyi na gano cewa zamana da humaira babu komai a ciki face takaici da damuwa....“ Na katseshi da karfi nace “FARUK!!“ ya daga min hannu da fadin ‘ HUMAIRA! minti daya.‘ ya dora da cewa “akwai cutarwa kwarai kmr yadda kake fada idan naci gaba da zama da humaira a haka kuma nima bazan so ta rayu har ta mu2 da bakin ciki ba don haka gata na dawo maka da ita har gida kmr yadda ka nema kuma zan tafi na.....“
.
Nayi saurin mikewa tsaye nayi dawurwura a guri daya naja da baya da sauri na fizgo wata sharbebiyar wuka na dan yanki hannuna kadan jini yayi tsartuwa kai tsaye na wuce da ita wuyana. daddy da momi suka mike da sauri tare da zaro ido, momi tadanyi kara da fadin “iohhh!!!!! humai...“ Faruk ya mike tare da cewa “humaira me kika dauka??“ Ba tare da tsoro ba nace “WUKA!! wuka ce faruk! kuma zan kashe kaina idan har ka tafi ka barni.“ Ya tako izuwa inda yake jin motsina ya tsaya cak a gabana yace “Karkiyi haka!! duk tsananin tashin hankali da ukuba kada kiyi yunkurin kashe kanki domin tashin hankalin da zaki tarar yafi wannan, zaifi ki nemi wata mafitar amma ba wannan ba. Ya miko hannunsa tare da cewa “bani wukar.“ Nabi fuskarsa da kallo wadda keda tasirin saurin sani ko hanani da kallo na saki wuka kasa na rike hannunsa nace “Karkayimin haka?? Nice fa humaira koka manta ne?? Kace ba zaka tafi ba don Allah kaji?? Kace da wasa kake faruk!! Ya banbare hannuna daga nasa yaja da baya yace “bakin alkalami ya bushe ba yadda muka iya, don kin rabu dani ba yana nufin shikenan ba. Kece dai humairar nan ta baya zaki samu wanda yafini kiyi rayuwar farin ciki. Ki manta da ba2na kawai ki dauka baki sanni ba a rywrki ki shimfida sbwr ryw, nina tafi.“ Ya kai karshen maganar ya juya ya nufi hanyar fita..
.
Natausayama faruq..!