Daya daga cikin dattawan Arewa Alhaji Tanko yakasai ya Bayyana Cewa Abu Daya Ne Ya Banbanta Mulkin Buhari Dana Fir'auna Saboda Shi Buhari Bai Bayyana Cewa Shi Allah Ne Ba, Amma Babu Mamaki Yana Shirye Da Ya Bayyana Hakan Saboda Duk Wani Mai Hankali Da Hangen Nesa Idan Ya Dubi Wannan irin Mulki Na Buhari Da Idon Basira Zai Ga Cewa Cike Yake Da Son zuciya Da Rashin Tausayi Saboda Talakawa Suna Cikin Ukuba da matsi na rayukawa tsawon watannin goma na mulkin Buhari.
Tanko yakasai ya kara da cewa komai ya tsaya cak a Nigeriya, rashin Kudi ya damu al'ummar Nigeriya, uwa uba shine shi ne karin farashin kayayyakin masarufi kullum kullum.
Dattijon Dan Nepu yakasai yaci gaba da cewa, Kara Farashin Abubuwa Kamar Irin Su kayan Masarufi Da kuma Karin Kudin Wutar Lantarki da karancin man fetur babban koma baya ne ga gwamnatin APC, Amma Kuma Shi shugaban kasa Buhari Babu Abinda Yakeyi Sai Yawo a Kasashen Duniya yake a cewar Yakasai.
Title :
Abu Daya Ya BamBanta Mulki Buhari Da Na Fir'una - Tanko Yakasai
Description : Daya daga cikin dattawan Arewa Alhaji Tanko yakasai ya Bayyana Cewa Abu Daya Ne Ya Banbanta Mulkin Buhari Dana Fir'auna Saboda Shi Buhar...
Rating :
5