A Gaban Idona Sojoji Suka Hallaka 'Yan Uwana Uku, Sannan Suka Harharbi Mahaifina Da Mahaifiyata, Inji Suhailat, Diyar Zakzaky
"Har Abada ba zan taba mancewa da rashin imani da tausayi da Sojojin Nijeriya suka aikata akan iyayena da 'yan uwana ba, lokacin da suka shigo cikin gidanmu dake Gyallesu Zariya, suka yi ta harbi ko'ina da ko'ina babu kakkautawa".
Wadannan kalamai, sun fito ne daga bakin diyar Zakzaky mai suna Suhailat Zakzaky, a yayin wani taron manema labarai, da Kungiyar Lauyoyi masu kare 'Yan Shi'a suka gudanar a cibiyar 'Yan Jaridu dake Kaduna.
Suhailat Zakzaky ta ci gaba da cewar, sojojin sun hauro cikin gidan nasu ne, bayan da suka yi nasarar karkashe daliban mahaifinta dake waje, sannan suka yi ta harbi a cikin gidan nasu babu kakkautawa, lamarin da ya yi sanadiyar rasuwar 'yan uwanta maza uku, sannan suka raunata mahaifinta da mahaifiyarta ta hanyar harbi, wanda yanayin harbin da suka yi wa nahaifanta ba su yi shi da niyyar su rayuwa ba.
Suhailat ta kara da cewar, bayan harbin da aka yi wa mahaifan nata ne, Sojoji suka kwashe su suka tafi da su, wanda tun daga wancan lokaci har ya zuwa wannan rana da muke ciki, sama da watanni uku, ba ta sake ji daga bangaren iyayenta ba, kuma ba ta sani ba suna raye ko sun rasu.
Tun farko da yake jawabi a wajen taron, shugaban Kungiyar Lauyoyi dake kare 'yan Shi'an Lauya Festus Okoye ya ce, babu dalilin da za su cibgaba da wakilta ko kare mutumin da ba su da masaniyar halin da yake ciki, shin yana raye ko ya mutu?
Title :
A Gaban Idona Sojoji Suka Hallaka 'Yan Uwana Uku, - Suhailat, Diyar El Zakzaky
Description : A Gaban Idona Sojoji Suka Hallaka 'Yan Uwana Uku, Sannan Suka Harharbi Mahaifina Da Mahaifiyata, Inji Suhailat, Diyar Zakzaky "Har...
Rating :
5