A yau Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Saudiyya.
A jawabin da mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan harkar yada labarai, Mista Femi Adesina ya fitar, ya bayyana cewa Buhari, wanda daga cikin tawagar da zai fita da su akwai karamin ministan man fetur, Ibe Kachikwu, da farko zai soma tattaunawa ne da Sarki Salman Bin Abdulaziz Al Saud da sauran manyan masarautar ta Saudiyya.
Ana zaton cewa shugabannin za su mayar da hankali ne kan batun farashin danyen mai a tsakanin kungiyar kasashe masu fitar da man fetur (OPEC) a tattaunawar da za su yi.
Haka kuma ana zaton za a yi tattauana ne kan matsalar faduwar farashin danyen man fetur a duniya, a yayin da shugaba Buhari ya je Doha babban birnin Qatar a ranar Asabar mai zuwa , inda zai gana da Sarkin kasar, Sheik Tamim bin Hamad Al Thani a washegari Lahadi.
Title :
Yau Buhari Zai Kai Ziyara Kasar Saudiyya
Description : A yau Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Saudiyya. A jawabin da mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan har...
Rating :
5