Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja a yau Juma'a zuwa kasar Masar, domin halartar wani taron harkokin kasuwanci na Afirka da Masar da kuma na kasashen duniya.
Taron wanda za'a bude shi a Masar din a gobe Asabar, gwamnatin Masar din ce ke shirya shi, karkashin hukumar Tarayyar Afirka.
Daga cikin wadanda za su gudanar da jawabai a taron sun hada da Shugaba Buhari da Shugaban Masar Abdel Fatah al sisi.
Sauran su ne shugabannin kasashen Togo, Sudan, Kenya, Gabon, Equitorial Gini da kuma Firaministan kasar Habasha.
Title :
Yau Buhari Zai Je Taro Kasar Masar
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja a yau Juma'a zuwa kasar Masar, domin halartar wani taron harkokin kasuwanci na Afirka da M...
Rating :
5