Y'AR AMANApart 3
** Ahankali taci gaba da ratsa kasaitaccen gdn nasu, kai tsaye ckn gdn ta durfafa hannunta rike da ledar siyayyar data yo.
Daga ina???
Kalaman da suka dira a kunnenta kenan kmr daga sama, tayi saurin dakatawa domin tadau muryar ko waye, kai tsaye takai kllnta ga inda taji anyi maganar tayi arba da Abbanta.
Tadanyi saurin sakin fuskarta tare da cewa " uhm!! Abba daga siyayya nake, momi ce ta aikeni."
Aiken ne sai yanzu?? Karfe kusan 7:00 na dare??
Ta danyi saurin cewa "Abba kudi ne suka yanke min don kusan a kasa ma na dawo." waye wancan daya saukeki a mota??
Yayi nuni izuwa waje da dan yatsansa. Tadan zaro ido kadan tare da tambayar kanta " dama ya ganshi?? " ta dago kai muryarta tadan kara canjawa domin tana gudun kar yaki fahimtarta duk da tasan saukin kansa, nan ta kwashe duk abinda ya faru ta fada masa.
Ya kara jefo mata tambayar " a gdnnan ba motoci?? "
kanta na kasa tace "direba ne bayanan kuma ya tafi da mukullan motar."
Y'AR AMANA ba zarginki nake ba amma kibi a hnkl ki kuma kula a duk inda kike, kinji ko??"
A hnkl ta gyada kai alamar amsa abnd ya fada mata ta kuma taka ta wuce izuwa ckn gdn yabita da kll kawai tare da grgz kai tamkar me tausaya mata.
Sannu Alhaji!! Wani dan lukutin mutumi fari ya fada ya wuce.
Yauwa!! zonan. Ya fada.
Da sauri mutumin ya dawo tare da risinawa ckn grmmw, gani alhaji. Alhaji jamil ya gyara babbar rigarsa tare da cewa "ina kaje dazu kabar aikinka alhalin kasan a matsayinka na direba kowanne lkc za'a iya nemanka??"
direban ya kara risinawa da fadin " ranka ya dade hajiya ce ta aikeni. "
menene dalilin tfy da mukullan motocin gdn to??
Ya kara tambaya ba tare daya kalleshi ba. Ita tace na tafi dasu.
Shiru kawai Alhaji jamil yayi kmr me tunanin wani abu, tbbs zata iya!! ya fada a ransa. Ya juyo gareshi yace " bazan hanaka kaje aikenta ba amma karka kara tfy da mukullan motocin gdn nan, sbd motocin ba naka bane kuma ba nata bane, nawa ne " yayi nuni da kansa.
Jeka!! Ya fada sanda shima ya juya tare da takawa ya nufi ckn gdn.
Tun kafin ya karasa yake jiyo sautin hajiyar tana bambamin bala'i ta inda ta shiga batanan take fita ba.
A hnkl ya karasa hamshakin falon alfarmar yana me binta da kll, kawai tasa Y'AR AMANA a gaba ta inda ta shiga ba tanan take fita ba.
Domin a cewarta wai taje ta zauna don taja mata zagi, harda sharrin wai siyayyar ma ba dai-dai tayo ba.
Ganinsa ne yasa tayi saurin dakatawa taci gaba da hura hanci.
Ya kikai shiru?? kici gaba mana, Ya fada yana me kllnta.
Ko kuma keda kanki kinsan ba adalci kike aiwatarwa ba ko??
Ba tare da bata damar amsawa ba ya dora da cewa "kin aiketa byn kin sani sarai direba bayanan kuma ke kika aikeshi kuma sbd mugunta sai kika bata kudi kai da kai da siyayyarki, sbd sanin yakamata irin nata bata rage miki komai a siyayyarki ba ta gwammace ta dawo a kasa, amma duk da hakan da fada zaki saka mata.
Kin kyauta.
Yakai karshen mgnr tare da duban inda y'ar amana ke zaune yace " tashi ki wuce kinji!! Allah yayi miki albarka." A hnkl ta mike tare da dan risinawa a gabanta tace " kiyi hakuri momi."
ta taka tare da wucewa izuwa dakin dake fuskartarsu." ya juyo da dubansa ga hajiyar da har yanzu fuskarta ke a daure tamau yace "yakamata ki rinka kamanta adalci a duk abinda zakiyi sbd kina nuna fifiko fiye da kima..."
Alhaji kenan bani da ikon aiken yarinyar nan ko nayi mata fada idan tayi min ba dai-dai ba?? Ta fada tare da kauda kai.
Kina dashi!! Ya fada tare da dorawa da fadin "amma ai ba ita kadai ce a gdnnan bako?? Ina farida??
To daga yau inda idan kin tashi aikenki ki aikesu su duka, idan sukayo ba dai-dai ba idan duka ma ta kama ki dakesu su duka amma baki aiketa ita kadai ba, kinji na fada miki."
ya juya tare da barin falon izuwa dakinsa. Tabishi da kll kawai, koba komai tasan hakan zai rage mata damar tozarta yar amana.
** barin falon da tayi kai tsaye ta fada dakinsu wanda su biyu kacal a cknsa, sallama tayi wanda ya samu amsawar isa da gadara daga farar kyakykyawar budurwar dake zaune a tsakiyar tafkeken gadon barci me matukar kyau da ban sha'awa tana karanta novel, y'ar amana ta karaso bakin gadon tare da zama bayan tace "kai! Rufaida na debo gjy da yawa wlh."
ai nayi mamaki naga tun dazu shiru.
Ta fada har yanzu bata dago kai ta dubeta ba.
Kedai bari kawai, kinyi salla kuwa??
Yar amana ta sake tambaya.
Nikam nayi kece dai makararriya.
Yar amana ta mike tare da cewa bari ki gani nima dai na tashi na daura himma kada lkc ya kara ja, kai tsaye ta nufi dauro alwala, rufaida tabi ta kallo ta baya kasa-kasa taja tsaki tare da cewa "banza wai ita Y'AR AMANA."
Cak! Ta tsaya tare da waigowa da cewa " me kika ce?? " rufaida ba wani canjawa da tayi tace "me nace kuwa?? Ni Ba abnd na fada."
yar amana taci gaba da kllnta kawai nadan lkc har idonta ya ciko da kwalla ta juya kawai izuwa inda ta dosa.
*tunda ta zauna zaman sallar bata tashi ba sai data dau wajen awanni biyu, ta hada harda sallar isha'i tayi nafilolin data saba sannan ta tashi ta koma kan gadon, har yanzu farida nanan rike da novel ta dukufa.
Gobe lakcar mu ta safe ce yakamata ki kwanta da wuri.
Yar amana ta fada sanda ta zauna a bakin gadon.
Rufaida tace "na sani." bakiyi sallar isha'i bama fa!! Ta sake fada tana duban rufaidar.
Zanyi!! Ta sake bada amsar a gajarce.
Yar amana ta mayar da zaman da tayi izuwa kwanciya tace "sai yaushe??"
rufaida ta kauda kai tare da cewa "kai!!" ta dawo da dubanta gareta tace "ina ruwanki??
Babu!!
Yar amana ta fada tare da gyara kwanciya ta juyar da kanta daga fuskantar rufaida.
Ta dade a haka ba tare da barci ya kwasheta ba, kwakwalwarta nata tariyo mata abubuwa daban-daban da suka faru yau har dai barci yayi awon gaba da ita.
** washe gari kmr kullum misalin karfe takwas na safe zaune suke su uku bisa kujeru sun zagaye makeken tebirin dake dauke da abinci kala-kala wanda yayi dai-dai da irinna break fast, kujera daya ce tak! Ba kowa akanta wato wacce Abbansu ke zama sai dai yau su uku suke yin break din ba tare dashi ba.
Shiru ne kawai ke gudana a wurin ba wanda ke cewa kowa komai, zuwa can yar amana ta dago kai kmr ta tuno wani abu tace " wai momi yau abba lfy naga bai fito ba har yanzu?? "
momin kmr ba zata ce komai ba zuwa can tace " lfyrsa qlau kawai baiyi niyyar fitowa bane. "
ta fada tare da kauda kai. Bari nagama naje na dubashi. Yar amana ta fada. Farida ta dago kai tare da cewa " ok! Baki yarda da abnd aka fada ba kenan ko?? "
nidai bance haka ba, shikenan ko yana da lfy bazan je na gaidashi ba?? Mahaifinane fa??
Y'ar amana ta fada.
Farida ta kalleta ta dauke kai tare da cewa " mahaifinmu dai... Bake kadai ba malama. "
yar amana tabita da kll kawai ta kauda kai tare da cgb da yin abnd ke gabanta. Jim kadan suka kammala su biyu suka mike suka doshi dakinsu tare da fara shirye-shiryen tfy makaranta don daukar laccarsu ta yau.
Tare suka fito izuwa falon kowaccensu ckn shiga irin tata kuma irin wacce ta sabayi, hajiyar ce kawai zaune a falon, yar amana ta dubi farida tace " ina zuwa bari na shiga na gaida Abba sai mu tafi. "
farida ta dubeta tare da duban agogon wayar dake hannunta tace " kinga nusaiba dalla kizo mu tafi mun kusan makara kin sani fa!! "
ba tare data saurareta ba ta fada dakin abbannasu.
Farida ta harareta tare da doka tsaki ta koma kan kujerar ta zauna tace " ni ban taba ganin banza irin wannan ba wai ita yar amana mtsss...."
meye na tsakin to??
Hajiya dake zaune ta fada.
Kawai haushinta nake ji wlh momi sbd munafuncinta. Farida ta fada.
Ba yar uwarki bace kike ce mata munafuka??
Haka dai ake cewa wai yar uwata ce amma allah momi ina kokwanton cewa anya kuwa ke kika haifi nusaiba??
Jifa fatarmu ni dake farare sol damu amma ita bakikkirin da ita."
amma ubanku ai baki ne ko?? Momi ta fada.
Tambayar da faridar ta kasa amsawa kenan ta shiga 2nani momin ta mike tabar falon.
** Y'ar amana kai tsaye ta wuce ga inda abbanta ke zaune bisa darduma byn tayi sallama ta zauna a gefensa nesa kadan, ya dago kai a hnkl tare da cewa "Y'AR AMANA".
Na'am Abba ina kwana?? Lfy qlau, ya amsa.
Shiru ya gudana nadan lkc tsakaninsu zuwa can ya katse shirun da cewa "yar amana da wani abu ne?? "
abba akwai.
Ta amsa wanda yasashi gyara zama da cewa " fadi mana yar amana. "
Abba tambayar nan ce dai dana saba yi maka a kowanne lkc wacce baka gamsar dani amsarta, don allah ka fada min wacece ni?? Meye alakata da wannan gdn??
Domin zuciyata da kasa yarda da cewa ni yar gdnnan ce, tbbs akwai wani boyayyen al'amari game da ni."
yayi saurin grgz kai tare da cewa " waye ya gaya miki?? Na dade da fada miki cewa "ki cire wannan 2nanin a ranki, ke y'ata ce kuma y'ar gdnnan gaba da baya ba wani lbr idan ba wannan ba." amma me yasa momi da farida keyi min haka?? Me yasa basa kaunata??
Kenan momi ba ita ce mahaifiyata ba?? In haka ne wacece??
abba ka taimakeni ka fada min don allah koda lbrn bazai min dadi ba nidai na fita daga rudani."
yadan bita da kll tare da kakalo murmushi yace " yar amana kenan, ba haka bane tana kaunarki sbd bata da kmrki kema kuma haka baki da wata mahaifiya idan ba ita ba, sai dai wata kila idan ni ina nuna miki kauna 100% ita sai ta nuna miki 90% don kar a shagwabaki da yawa."
Yakai karshen maganar dashi kansa yasan ba haka take ba. Ta dago kai tare da cewa " to abba me yasa kake cemin yar amana idan har kaine ka haifeni?? " ya danyi shiru domin jin tambayar yayi kmr daga sama zuwa can yayi murmushi tare da cewa " yar amana dukkan da ko y'a amanar allah ce don na fada miki haka bana jin akwai wani abu." da amsoshin dashi kansa me bada su ya tbbtr ba gamsassu bane ta mike tare da cewa "abba zamu tafi makaranta sai mun dawo."
to a dawo lfy allah ya tsare, komai dai lfy ba wata matsala ko?? Ta grgz kai kawai alamar babu ta wuto izuwa waje, farida bata falon abnd ke nuni da 2ni ta kosa tayi waje, jakarta kawai ta zara tayo waje kai tsaye izuwa harabar gdn ta fito 2ni kuwa direban ya seta motar ta fuskanci waje ita kawai suke jira.
Da sauri ta bude motar ta shiga ta mayar ta rufe tare dace musu "am sorry fa na tsaida ku ko?? Mu tafi."
ta fada tare da duban direban.
A hnkl ya taka motar suka fice farida nata harararta da gefen ido.
Tayi kicin-kicin ta hade rai tamkar bata taba yin dariya ba, direban da yar amana ne kawai keyin hira jefi-jefi. Ba kuma yanzu kawai ba kusan kowanne lkc yar amana ce kawai ke iya sakin fuska da kuma yin hira da ma'aikatan gdn sabanin farida da kowanne lkc fuskarta ke a daure bawai ga yan aikin gdn nasu ba ga kowa ma, hakan yaja mata bakin jini a wajen al'umma.
Yar amana ce yar gaban goshi a wajen kowa sbd kyawawan halayenta da iya zama da kowa, tana da farin jini a wajen jama'a musamman a makarantarsu sunanta ya zagaye ko ina, duk inda kayi yar amana ake fada wanda hakan ke kona ran farida a ko yaushe.
Anya ko bawani abu aqasa???
Barkan ku da yamma..injiAßdool-azeez ßeen Aßoußakar
Dan samun rubu tun mu akoda yaushe