Saurayin tsayawa kawai yayi yana kllnta ba tare da yace komai ba, ya dan dauki tsawon sakwanni kadan kafin ya gyara tsayuwarsa fuskarsa bata wani nuna alamun damuwa ba ko kadan.
Ya sake binta da kallo tare da cewa " haba BAIWAR ALLAH!! Me yayi zafi haka??
Sanin cewa nayi miki laifi fa shi yasa ma na dakata don baki hakuri, amma kin kama zagina idan kuma nima nahau sama me kike zaton zai faru??
Fada zamuyi kenan??"
ya saisaita muryarsa ckn rarrashi da cewa: "Don Allah kiyi hakuri, hanyar ce da ramuka da yawa su nayi kokarin kaucewa ko kadan ban lura da wannan ba.
Kiyi hakuri"
ya sake mai-maitawa a karo na biyu.
Lkc guda jikinta yayi sanyi domin ta tbbtr da cewa ba yadda tayi zato yake ba, tbbs bai cancanci bakaken maganganun data fada masa ba.
dakyar ta iya dago kai ta dubeshi tadan jinjina kai alamar amsa abnd ya nema, kamar me jin kunyar magana kuma tace " nayi gaggawar yanke hukunci ckn fushi ba tare da nayi maka uzuri ba raina ne ya baci amma kayi hakuri..."
Daga ganinki bakiyi kama da mara hakuri ba, sai dai kowacce zuciya kanji zafi duk sanda aka munana mata nagode da fahimta ta da kikai.
Ya taka zai wuce idonsa yakai ga jikinta a karo na biyu, ba karamin bata ta yayi ba hakan yasa ya dakata tare da juyowa gareta yace " idan ba damuwa ki shiga mota na karasa dake gida mana. "
Tayi saurin grgz kai da cewa " A'A ngd kaje kawai zan karasa."
Yadanyi murmushi tare da cewa " bai dace ki tafi a haka ba koda namiji ne bare ke mace, zai fi kyau na direki har kofar gdnku yadda ba wanda zai ganki a haka."
Ta sake grgz kai da cewa "ka riga ka bani hakuri kuma na hakura, na shiga motarka kuma ba abune me karbuwa ba kayi hakuri kawai."
Takai karshen maganar sanda ta juya taci gaba da tfy bisa mikakkiyar hanyar. Binta da kll kawai yayi da sauri yace "hakan na nufin baki hakura ba kenan??"
Tayi saurin dakatawa da tafiyar tare da juyowa tace " ba haka bane!..."
Idan har kin hakura da gaske to ki bani dama na kyautata miki sau daya tak!! " ya fada byn daya katseta.
Kmr zata ce wani abu amma ta fasa wanda ya bashi damar takowa da fadin " idan kuma kina zaton ni wani mugun ne to ki cire hkn daga ranki don na tbbtr idanuna kawai sun isa sheda akan cewa ni bame yanka kan mutane bane."
dariya tadan kwace mata sanda ta taka suka jera tace " su din ai ba kama garesu ba.
" eh hakane amma ki yarda dani ba wani mugun nufi a tare dani.
Ta gyada kai da cewa " da ganinka kam, amma kasan a matsayina na mace dole nayi taka tsan-tsan ko?? Sbd mutum abin tsorone musamman maza. Ta fada dai-dai sanda suka karaso jikin motar tasa.
Yayi dariya tare da cewa " wasu ba amma duk lalacewa akwai nagari."
ya bude kofar motar ya shiga tare da bude mata kofar gaban daga ciki, ba tare da gardama ba ta kuwa shiga tare da mayar da kofar ta rufe.
Wani iri taji domin yaune ranar farko data aminta da shiga motar wanda bata sani ba, shigar tatane kuma ya kara tbbtr mata motar ta kasaita ce domin daga ciki ya linka wajenta kyau ma2ka ga sanyin A-C ta ko ina.
A hnkl ya fara 2ka motar ckn nutsuwa tana meyi masa nuni da hanyar gdnnasu, sai da suka dauki tsawon lkc suna tfy zuwa can yana me duban hnyr yace " gdnku nada nisa ashe amma me yasa tunda wuri baki nemi taxi kin hau ba??
Tadanyi yake ckn muryarta mara amo tace " eh! Daga siyayya nake a AGH STORE, mahaifiyatace ta aikeni to kaga kudin data bani da naje sai naga abbwn data lissafa min da kudin hannuna sunzo kai da kai.
Idan har inaso nayi kudin mota to sai dai na rage wani abu daga siyayyar ni kuma bana so nayi mata haka, shine kawai na gwammace nayi mata siyayyarta gaba daya na koma a kafa."
Da sauri ya dubeta nadan lkc sannan yace " Allahu akbar!! Kin fifita bukatar mahaifiyarki akan taki!! Kin yarda kisha wahala ki shiga tsanani don farantawa mahaifiyarki!!
Irinku a duniya kadan ne, Allah ya bani irin halinki koda ba duka ba. Ta danyi dariya tace " wace ni?? Ai halinka yafi nawa nesa ba kusa ba."
me yasa kika ce haka?? Ya tambaya. Ta gyara zama tace " akwai hadisin dake cewa:
[mafi alkhairi a ckn mutane shine wanda aka batawa yana da damar daukar mataki amma ya hakura]
amma ni da kayi min laifi sai na kasa hakura nadau matakin da shine iyakar abnd zan iyayi, kaga kai kuma duk da na bata maka da munanan kalamai sai baka dau mataki ba ka hakura harma ka taimakeni.
Kaga kenan kana daga ckn mafi alkairi a ckn al'umma."
ya danyi murmushi kadan da cewa " kuma dai ashe ke yasayyada ce??"
sukayi dariya dukkansu.
Tafiya kadan suka kara suka iso wata kasaitacciyar unguwa kll daya zakayi mata kasan ungwr masu akwai ce.
Mun iso!! Ta fada.
Yabita da kll tare da taka birki motar ta tsaya cak!! Ya dubeta "to Amma dai yakamata nasan sunanki domin nasan ba lallai mu sake haduwa ba."
Ta danyi murmushi da cewa " sunana nusaiba jamil amma anfi kirana da sunan Y'AR AMANA."
ya danyi shiru zuwa can ya maimaita sunan "Y'AR AMANA!!
Kmr akwai inda nake jin sunan nan."
ta yiwu amma sai dai wata daban bani ba.
Ta kama kofar tare da budewa ta juyo tace " bazan taba manta abnd kamin ba, laifi daya tak! Amma kabi hnyy da yawa na faranta min ngd sosai mlm....." USMAN!!
Ya karasa mata.
Usman itama ta fada tare da dorawa da fadin "ngd sosai".
ta bude kfr ta fice yabita da kll yana murmushi sai dai fskrs ta sauya da yaga katafaren gdn data shiga, ya hango motocin alfarma a hrbr gdn, ckn grmmw kuma me gadi ya bata hny ta wuc abnd ke nuni da cewa yar gdnce.
To amma idan hkne me yasa ba za'a dauketa a mota a kaita ba??
Irin tmbyyn da fara yiwa kansa kenan, Y'AR AMANA ya sake fada kfn ya taka mtrsa ya tafi...
Uhmm wato ya shiga kenan...allah sadai baxakakasa fitaba...
Kunsan shi love shegen abune,,
Aßdool-azeez ßeen Aßoußakarke muku barka da asubah..
Dan samun rubu tun mu akoda yaushe shigo nan