DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
A zaman da Kwamitin bincike kan rikicin 'yan Shi'a da rundunar Sojoji ya gudanar a yau Litinin, a gidan gwamnati na Hassan Katsina dake Kaduna, 'yan Shi'a ba su halarci zaman kwamitin ba, wanda ya lashe tsawon sa'o'i yana zama.
Lokacin da yake jawabi gaban manema labarai jim kadan bayan kammala zaman Kwamitin, Lauyan Kungiyar Jama'atu Nasril Islam mai suna Barista Muhammad Sani Katu, ya ce sun samu sanarwa daga wajen Lauyan 'yan Shi'a cewa, 'Yan Shi'a ba za su halarci wannan zama ba, har sai idan sun samu izini daga wajen Jagoransu Sheik Zakzaky, kasancewar ba su aikata komai sai bisa ga yarda umarnin shi.
Daga karshen zaman Kwamitin, ya dage zaman sauraren ya zuwa ranar Laraba, domin tattauna yiyuwar ganawar 'Yan Shi'an da jagoran nasu Zakzaky, domin samun halartarsu zaman na gaba, kasancewar dukkanin sauran bangarorin jama'a tun daga kan Sojoji da sauran jama'ar gari sun halarci zaman na yau.
Title :
Yan Shi'a Sun Ki Halartar Zaman Kwamitin Binciken Gwamna El Rufa'i
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA A zaman da Kwamitin bincike kan rikicin 'yan Shi'a da rundunar Sojoji ya gudanar a yau Litinin, a gida...
Rating :
5