DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA
A zaman da Kwamitin bincike kan rikicin 'Yan Shi'ah da Rundunar Sojin Nijeriya wanda Gwamna Nasiru El Rufa'i ya kafa ya yi a yau Laraba a gidan Gwamnatin Jihar na Hassan Katsina dake Kaduna, ya saurari korafi wanda Lauyan dake kare 'Yan Shi'a mai suna Barista Maxwell Kyon ya gabatar, inda ya bukaci Kwamitin ya kara masa wa'adin makonni biyu domin ya samu damar ganawa da jagoran mabiya Shi'a a Nijeriya Malam Zakzaky wanda ke tsare.
Saidai nan take Lauya dake kare Sojin Nijeriya Barista Abba Audu da Lauyan gwamnatin tarayya Barista Ishaq Yunus, sun soki lamirin Lauyan 'Yan Shi'an, inda suka ankarar da Shugaban Kwamitin binciken Mai Shari'a Muhamma Lawal Garba, akan cewa Kwamitin bayada isasshen lokacin zama, domin Makwanni Shidda akaba Kwamitin daya kammala zama ya kuma mika rahotonshi, a domin haka ya kamata a kiyaye dangane da batun daga zaman Kwamitin.
Daga karshen zaman Kwamitin a yau, Shugaban Kwamitin Mai Shari'a Muhammad Lawal Garba, ya dage zaman Kwamitin har ya zuwa ranar Litinin wato 29 ga watan Fabarairu, domin cigaba da sauraran korafe-korafen.
Title :
Yan Shi'a Sun Kauracewa Zaman Kwamitin El-Rufa'i A Karo Na Biyu
Description : DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA A zaman da Kwamitin bincike kan rikicin 'Yan Shi'ah da Rundunar Sojin Nijeriya wanda Gwamna Nasiru El ...
Rating :
5