Mazauna unguwar Jiwa dake babban birnin tarayya Abuja sun shiga cikin mamaki a yayin da suka ji labarin ana shirin daura auren jinsi a yankin.
Wadanda suke shirin yin auren masu suna Abdul Lawal da Umar Tahir, wadanda bincike ya nuna cewa dukkansu 'yan asalin jihar Kaduna ne, sun kwana ne a wani otal a garin na Jiwa, inda ake sa ran za a daura auren a washegari.
Bincike ya nuna cewa har wurin da za a daura auren ya cika da manyan bakin da aka gayyata tare kuma da kawata wurin. Sannan kuma ango da amarya sun iso wurin da za a gudanar da shagalin bikin, sai ga tawagar 'yan sanda inda suka yi awon gaba da ango da amayan.
Majiyarmu ta kara da cewa, baya ga ango da amarya da aka kama, an kuma kama manyan bakin da aka gayyata wurin daurin auren.
Ofishin 'yan sanda na garin Gwagwa sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka kara da cewa tuni aka mika su ga sashen binciken manyan laifuka.
Title :
Yan Sanda Sun Kama Wasu Da Suke Shirin Yin Auren Jinsi A Abuja
Description : Mazauna unguwar Jiwa dake babban birnin tarayya Abuja sun shiga cikin mamaki a yayin da suka ji labarin ana shirin daura auren jinsi a yank...
Rating :
5