Daga Sani Musa, Abuja
Bincike da wakilin mu ya gudanar a wasu majalisun kananan hukumomin jihar Nasarawa, ya nuna cewa direbobi dake kananan hukumomin sun nanka yawan motoci da ake da su.
Ga misali a karamar hukumar Nasarawa wadda mota daya ce kawai take aiki tana da direbobi kusan 40, haka ma lamarin yake a Karu, Keffi, Toto da kuma Kokona.
Wani ma'aikacin karamar hukumar Nasarawa wanda ya ce an dauke shi aiki ne a matsayin direba, amma ba ya aikin komai, sai dai ya jira albashi kawai, ya ce yau kusan shekara biyar kenan ba ya zuwa ofis saboda koda yaje babu mota da zai yi aiki da ita.
Binciken ya kuma gano cewa a wasu kananan hukumomin motacin shugabanin kananan hukumomin ne kawai ke aiki Amma suna da direbobi masu yawan gaske wadanda suke karban albashi a duk wata.
Wakilin namu ya ruwaito mana cewa wasu daga cikin direbobin suna sa,ar aikin kabu kabu ne kuma suna a matsayin ma,aikata.
Wannan abun ya fara jawo cece kuce tsakanin shugabanin kananan hukumomin jihar da kuma kungiyar ma'aikatan kananan hukumomin ta Nijeriya NULGE reshen jihar, inda Shugabanin ke bukàtar a rage yawan dirobobin saboda basu aikin komi ita kuwa NULGE ta ce ba za ta saku ba wai bindiga a ruwa.
A yanzu haka ma dai mai'aikatan jihar ta Nasarawa suna cikin yajin aiki na kusan wata daya kenan suna son gwanati ta biya masu wasu bukatun su a ciki harda karin girma,daukar karin ma,aikata tare da daina biyan ma,aikatan kananan hukumomi albashi rabi da rabi.
Title :
Yadda Direbobin Ma'aikatun Kananan Hukumomin Jihar Nassarawa Suka Ninka Motocin Da Suke Amfani Da Su
Description : Daga Sani Musa, Abuja Bincike da wakilin mu ya gudanar a wasu majalisun kananan hukumomin jihar Nasarawa, ya nuna cewa direbobi dake kanan...
Rating :
5